Ayyuka 774,000: Jerin sunayen bankuna 6 da za su budewa ma'aikata asusu - FG

Ayyuka 774,000: Jerin sunayen bankuna 6 da za su budewa ma'aikata asusu - FG

- Duba da karatowar lokacin fara diban ma'aikata na musamman a karkashin kungiyar kwadago da ayyuka, gwamnatin tarayya ta fara shiri

- Gwamnatin tarayya ta mika wasiku ga bankuna 6 domin fara bude asusun bankuna ga wadanda za su yi ayyukan na musamman

- Hatta a kananan hukumomin da basu da reshe, za su bude rassa na wucin-gadi domin saukake wa jama'a tafiye-tafiye

Kafin fara diban ma'aikata na musamman, gwamnatin tarayya ta mika wasiku ga a kalla bankuna shida domin bude asusu ga wadanda za a diba ayyukan.

Karamin ministan kwadago da ayyuka, Festus Keyamo, ya bayyana hakan a wallafar da yayi a shafinsa na Twitter, ya ce bankunan za su bude rassa na wucin-gadi a wasu kananan hukumomi da babu su.

Kamar yadda minsitan yace, bankunan sune: Zenith, UBA, Access, Fidelity, FCMB da Heritage, kuma gwamnati za ta sanar da bankunan kowacce karamar hukuma.

"Na bada wasiku ga bankuna shida domin fara bude asusu ga wadanda za su yi ayyuka na musamman na gwamnatin tarayya a fadin kananan hukumomi 774 a kasar nan.

“Bankunan sun tabbatar da cewa, ko a kananan hukumomin da basu da rassa, za su bude na wucin-gadi saboda samar da sauki ga masu bude asusun bankin. Za mu fitar da sunayen bankuna na kowacce karamar hukuma," ministan yace.

KU KARANTA: Nufin Allah: Dattijuwa ta zama cikakkiyar likita tana da shekaru 50 (Hotuna)

Ayyuka 774,000: Jerin sunayen bankuna 5 da za su budewa ma'aikata asusu - FG
Ayyuka 774,000: Jerin sunayen bankuna 5 da za su budewa ma'aikata asusu - FG. Hoto daga @Dailytrust
Source: Twitter

KU KARANTA: Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna)

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai yuwuwar tarwatsewar Najeriya idan ba'ayi kokarin toshe barakar dake kunno kai ba.

Yace akwai wadanda zasu iya yunkurin hana toshe barakar, amma idan aka jajirce kuma aka dage da addu'a za'a iya cimma gaci.

Osinbajo yayi wannan jan kunnen ne a ranar Lahadi a Abuja a wata tattaunawa da aka yi da shi, saboda shiryawa shagalin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai na Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel