Ba mu samu umarnin janye karin kudin wutar lantarki ba - DisCos

Ba mu samu umarnin janye karin kudin wutar lantarki ba - DisCos

- DisCos, wato kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki a kasa, sun ce ba su samu umarnin dakatar da sabon karin kudin wuta da su ka yi ba

- A ranar Litinin ne kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da gwamnatin tarayya (FG) su ka kulla yarjejeniyar jingine yajin aiki

- NLC ta amince da jingine yajin aikin ne bayan FG ta yi alkawarin cewa za a dakatar da sabon karin kudin wutar lantarki

Kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki (DisCos) da ke Najeriya sun bayyana cewa basu samu umarnin dakatar da karin kudin wutar lantarki da suka yi ba a farkon watan Satumba.

An cimma yarjejeniyar janye shiga yajin aiki a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago (NLC) bayan gwamnati ta amince cewa za a dakatar da karin kudin wutar lantarki.

Sai dai, kwana daya bayan NLC ta sanar da janye yajin aikin, DisCos sun ce basu samu wani sako daga FG ba dangane da dakatar da sabon karin kudin wutar lantarki.

DUBA WANNAN: Kano: Kotu ta zartar da hukuncin daurin wata bakwai a kan mashayin tabar wiwi

A ranar 1 ga watan Satumba ne DisCos su ka fitar da sanarwar cewa za su fara aiki da sabon tsarin cajin kudin wutar lantarki (SRT) a fadin kasa.

Ba mu samu umarnin janye karin kudin wutar lantarki ba - DisCos
Ganawar NLC da shugabancin majalisa
Source: UGC

Wani jigo a kungiyar ANED, wacce itace kungiyar da ta hada dukkan DisCos da ke Najeriya, ya sanar da jaridar TheCable cewa har yanzu DisCos ba su samu umarnin dakatar da sabon karin da suka yi ba.

DUBA WANNAN: Sabbin alkalan kotun koli: Buhari ya aikawa majalisa sunayen mutanen 8

"Har yanzu DisCos basu samu wani umarni daga NERC ba a kan dakatar da karin kudin wutar lantarki.

"FG da NLC sun tattauna tare da kulla yarjejeniya, amma umarnin NERC ne kadai zai sa DisCos su dakatar da karin. Har yanzu shiru, ba su aiko da kowanne sako ba," a cewar jami'in ANED.

An dakatar da karin kudin wutar lantarki ne na tsawon sati biyu yayin da kwamitin FG zai duba dalilin yin karin kudin tare da daukan matsayar amincewa da karin ko akasin haka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel