Nufin Allah: Dattijuwa ta zama cikakkiyar likita tana da shekaru 50 (Hotuna)

Nufin Allah: Dattijuwa ta zama cikakkiyar likita tana da shekaru 50 (Hotuna)

- Wata mata mai suna Nya Syndab, ta wallafa hotunan mahaifiyarta tare da labarinta mai ratsa zuciya

- Syndab ta bayyana cewa mahaifiyarta ta kammala karatunta na jami'a inda ta zama cikakkiyar likta a shekaru 50

- Labarin dattijuwar matar ya bai wa jama'a masu tarin yawa babban kwarin guiwa kuma wallafar ta bazu

Nya Syndab budurwa ce kyakyawa da ta yi wallafar da ta dinga zagaye kafafen sada zumuntar zamani. Ta wallafa hotunan kyakyawar mahaifiyarta.

Syndab ta bayyana cewa, burin mahaifiyarta ya cika inda ta zama likita tana da shekaru 50.

A yayin wallafar, matasiyar budurwa ta wallafa kyawawan hotunan ta tare da mahaifiyarta inda tace, "Mahaifiyata ta zama likita tana da shekaru 50. Babban burnita ya cika. Ina tayata murna!"

Wadannan hotunan tare wallafar sun janyo cece-kuce. Jama'a masu tarin yawa sun dinga taya matar murna tare da diyarta.

KU KARANTA: Tun farkon mulkin Buhari, ba a fara da sa'a ba - Oyegun ya bayyana manyan kalubalen APC

Nufin Allah: Dattijuwa ta zama cikakkiyar likita tana da shekaru 50 (Hotuna)
Nufin Allah: Dattijuwa ta zama cikakkiyar likita tana da shekaru 50 (Hotuna). Hoto daga @NyaSyndab
Source: UGC

KU KARANTA: Ka shirya yajin aikinka da kanka - Hadimin Buhari ya caccaki Shehu Sani

A wani labarin na daban, An kirkiri jirgin sama na farko a tarihi dake amfani da sinadarin Hydrogen kuma har an tashe shi a sararin samaniya.

Jaridar How Africa ta wallafa yadda aka kaddamar da wani jirgin sama mai amfani da sinadarin Hydrogen a ranar 24 ga watan Satumba, a sararin samaniya a Bedfordshire da ke Ingila.

Kamfanin ZeroAvia, sune suka fara kirkirar jiragen saman dake amfani da sinadarin Hydrogen don siyarwa a cikin shekaru 3.

Val Miftakhov, shugaban kamfanin yace yana fatan wadannan jiragen zasu maye gurbin jiragen sama dake amfani da mai.

Ya ce, "Muna kokarin ganin cewa mun maye gurbin injinan jiragen sama masu amfani da mai,da injinan hydrogen".

"Mun tabbatar da munyi wa jiragen tsari ta yadda ba za su bari sinadarin yana fita ba, sannan za'a samu damar cika wa da zarar ya kare," cewar sa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel