Gwamnatin Katsina za ta bude makarantu a ranar 5 ga watan Oktoba

Gwamnatin Katsina za ta bude makarantu a ranar 5 ga watan Oktoba

- Gwamnatin jihar Katsina ta ce daliban frimare da sakandare na jihar za su koma makaranta ranar 5 ga watan Oktoba

- Sanarwar ta fito ne daga bakin kwamishinan ilimi na jihar Badamasi Lawal a ranar Talata 29 ga watan Satumba

- Lawal ya ce za a raba lokacin da daliban za su rika zuwa makarantar kana gwamnati za ta tanadi matakan kare yaduwar korona

Gwamnatin jihar Katsina ta ce makarantun gwamnati da masu zaman kansu na frimare da sakandare za su koma karatu a ranar 5 ga watan Oktoban 2020.

Kwamishinan ilimi na jihar Badamasi Lawal ne ya bada wannan sanarwar a ranar Talata a Katsina kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Za a bude makarantun Katsina a ranar 5 ga watan Oktoba
Aminu Bello Masari. Hoto @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jawabin rabuwar Najeriya: Dattawan Arewa sun gargadi mataimakin shugaban kasa Osinbajo

Kwamishinan ya ce za a fara yi wa daliban bita don jarrabawar zango na biyu daga ranar 5 ga watan Oktoba zuwa 16 ga watan yayin da za a fara jarabawar zango na biyun daga ranar 19 zuwa 23 ga watan Oktoba.

Lawal ya kara da cewa dalibai za su koma zangon karatu na uku daga 26 ga watan Oktoban 2020 zuwa 24 ga watan Janairun 2021 yayin da za a fara jarabawar zango na uku daga ranar 25 ga watan Janairu a kuma kammala ranar 5 ga watan Fabrairun 2021.

Ya ce dole dalibai da malamansu su rika saka takunkumin fuska a harabar makaranta su kuma rika bada tazara a tsakaninsu da kiyayye sauran dokokin dakile yaduwar COVID 19.

Ya kara da cewa gwamnati za ta yi feshin magunguna a makarantar sannan ta samar da abubuwan wanke hannu da na'urar gwada zafi/sanyin jiki don gane masu zazzabi mai zafi.

KU KARANTA: 'Yan sintiri ga FG: A shirye muke mu kawar da 'yan ta'adda da 'yan bindiga

Har wa yau, kwamishinan ya ce za a raba daliban ne rukuni zuwa rukuni, ajin frimari daya zuwa uku za su zo makaranta daga karfe 7.30 na safe zuwa 12.30 na rana yayin da aji daya zuwa shida na frimari za su fara aiki daga 12.30 na ranar zuwa 5.30 na yamma.

Lawal ya yi bayanin cewa masu zuwa jeka ka dawo a makarantun sakandare da na kwana za su rika zuwa makaranta karfe 7.30 na safe su tashi zuwa 12.30 na rana ga wadanda ke bangaren karamar sakandare.

Wadanda ke sashin babban sakandare kuma za su shiga makaranta daga 12.30 na ranar su tashi karfe 5.30 na yamma a cewarsa.

A wani rahoton, dan majalisa mai wakiltar Oyo ta Arewa, Sanata Abdulfatai Buhari ya ce zai goyi bayan jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu idan ya nuna sha'awar fitowa takarar shugabancin kasa a Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin hirar da ya yi da wani dan jarida, Edmund Obilo a ranar Alhamis kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel