Sabbin alkalan kotun koli: Buhari ya aikawa majalisa sunayen mutanen 8

Sabbin alkalan kotun koli: Buhari ya aikawa majalisa sunayen mutanen 8

- Shugaba Buhari ya aikawa majalisar dattijai sunayen mutane takwas domin amincewa dasu a matsayin alkalai a kotun koli

- A makon jiya ne wata kotu ta bayyana cewa Buhari ya saba ka'ida wajen nadin alkalan kotun koli

- Buhari ya sha suka a kan nadin alkalan kotun koli daga wurin 'yan Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aikawa majalisar dattijai sunayen mutane 8 domin amincewa da su a matsayin sabbin alkalan kotun koli.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ne ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aika yayin zaman majalisa na ranar Talata.

Hukumar kula da bangaren shari'a (NJC) ta amince da sunayen manyan alkalan da shugaba Buhari aikawa majalisar dattijai, a cewar Sanata Lawan.

Sunayen mutanen da Buhari ya aika sun hada da; Lawal Garba (arewa maso yamma), Helen Ogunwumiju (kudu maso yamma), Abdu Aboki (arewa maso yamma) da M M Saulawa (arewa maso yamma).

DUBA WANNAN: Batagari sun kaiwa jami'an kwastam harin kwanton bauna bayan sun kwace shinkafa

Ragowar sune; Adamu Jauro (arewa maso gabas), Sauel Oseji (kudu maso kudu), Tijani Abubakar (arewa maso gabas), da Emmanuel Agim (kudu maso kudu).

Sabbin alkalan kotun koli: Buhari ya aikawa majalisa sunayen mutanen 8
Buhari da Lawan
Asali: Twitter

Kazalika, shugaba Buhari ya aikawa majalisar dattijai sunayen mutane biyu da ya ke burin nadawa a matsayin jakadun Najeriya a kasashen waje.

Mutanen sune; Muhammad Manta daga jihar Neja da Yusufu Yunusa daga jihar Yobe.

DUBA WANNAN: APC ta yi babban rashi, tsohon gwamna ya sake komawa tsohuwar jam'iyyarsa PDP

A cewar Buhari, mutanen biyu za su maye gurbin Air Commdore Peter Gana (mai ritaya) da Alhaji Yusuf Muhammad wadanda a baya aka aika sunayensu zuwa majalisar dattijai domin tantancewa.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wata babbar kungiyar da ke rajin tabbatar da daidaituwar al'amura bayan annobar korona (ASCAB) ta bayyana cewa ta bankado tiriliyan N94.3 da aka karkatar da su ta hanyar kin sakasu a asusun kasa.

ASCAB, wacce ta hada kungiyoyin 'yan gwagawarmaya guda 70 ta sanar da hakan ne a cikin wata wasika da ta aikawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel