Durkusawar budurwa a gaban saurayi don karbar tayin aure ya janye cece-kuce

Durkusawar budurwa a gaban saurayi don karbar tayin aure ya janye cece-kuce

- Wata budurwa 'yar Najeriya ta tsugunna kasa ta amshi zoben sa rana a hannun saurayin ta

- Ba'a kai mako uku ba da wata budurwa daban ta tsugunna don amsar zoben sa ranar auren

- Mutane da dama sun ta cece-kuce akan fitar hotunan wadannan 'yan mata guda biyu

Ba'a ritsa mako biyu ba da wata budurwa ta tsugunna har kasa don amsar zoben sa ranar auren ta, wata budurwa ma ta bi sahun ta.

Wata budurrwa, Angel Nwedo, ta wallafa hoton sa ranar aurenta cikin farinciki.

Maimakon saurayin ya tsugunna ya mika mata zobe kamar yadda aka saba, kawai sai ga budurwar a kasa tana amsar zoben cike da annashuwa.

Wannan al'amarin yazo ne babu dadewa bayan hotunan wata budurwa mai suna Adaeza Gift Okolie, sun karade kafar sada zumunta.

Wanda ta tsugunna cike da annashuwa tana amsar zoben sa rana daga hannun saurayinta, yana tsaye.

Ta wallafa hotunan a shafinta da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda take bayyanar da farincikinta.

Kamar yadda Okolie ta wallafa, saurayinta sarkin mulkin zuciyarta ne, don haka bata ga dalilin da zai hana ta durkusa mishi ba.

Bayyanar hotunan sun jawo cece-kuce, inda har wasu ke ganin ta zubar da ajinta a matsayin mace, yakamata ta tsaya ya miko mata kamar yadda aka saba.

Wasu kuma suka yita yabonta, har suna ganin za ta yi biyayya a gareshi idan har ya aureta.

Har wasu na ganin yayi dace, saboda matan yanzu girman kai yayi musu yawa.

KU KARANTA: Katsina da Zamfara: 'Yan bindiga 32 sun shiga hannu, an kashe 1 - DHQ

Durkusawar budurwa a gaban saurayi don karbar tayin aure ya janye cece-kuce
Durkusawar budurwa a gaban saurayi don karbar tayin aure ya janye cece-kuce. Hoto daga Nwedo Angel
Source: Facebook

KU KARANTA: Magidanci ya halaka kwarton matarsa bayan kama su da yayi suna lalata a kan gadonsu na aure

A wani labari na daban, a cikin ranakun karshen makon da ya gabata ne aka yi shagalin bikin hadimi na musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin yada labarai, Bashir Ahmad.

Matashin hadimin shugaban kasar ya aura rabin ransa, Naeemah Junaid Bindawa a jihar Katsina.

Bayan kamun da aka yi a ranar Juma'ar da ta gabata, an daura aure kamar yadda addinin Islama ya tanada a ranar Asabar a Masallaci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel