An zargi Shugabannin kwadago da yaudarar ‘Yan Najeriya kan yajin aiki

An zargi Shugabannin kwadago da yaudarar ‘Yan Najeriya kan yajin aiki

- Cibiyar CHRICED ta yi Allah-wadai da janye yajin-aikin da aka yi jiya

- Shugaban cibiyar ya ce shugabannin TUC da NLC sun saida Ma’aikata

- Dr. Zikirullahi ya ce ‘Yan kwadago sun dade su na yaudarar al’umma

Cibiyar CHRICED da ke kare hakkin Bil Adama ta yi watsi da uzurorin da kungiyoyin NLC da TUC su ka bada na janye yajin-aikin da su ka shirya a da.

Babban darektan cibiyar, Dr. Ibrahim Zikirullahi ya maida martani a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba, 2020, bayan kungiyoyin sun fasa yin yajin.

Ibrahim Zikirullahi ya ce ba su goyi-bayan tafiya yajin-aikin da wasa ba, domin kuwa zuwa yajin zai taimaka wajen sa gwamnati ta dawo cikin taitayinta.

KU KARANTA: Kungiyar ASUU ta janye yajin-aiki?

Zikirullahi ya ke cewa da yajin-aikin ne za a nunawa gwamnati ba a yarda da manufofin ta ba.

A cewar shugaban wannan cibiya mai zaman kanta, kungiyoyin kwadago sun saida ‘yan Najeriya a matsayar da su ka cinma da gwamnati a farkon makon nan.

Ya ce:

“Abin kunya ne shugabannin kwadago biyu da tarihi ya sani da gwagwarmaya domin kare martabar ‘yan Najeriya sun koma karbar tayin zama a kwamitin gwamnatoci.”

An zargi Shugabannin kwadago da yaudarar ‘Yan Najeriya kan yajin aiki
Shugabannin kwadago da Femi Gbajabiamilla Hoto: Daily News
Asali: UGC

KU KARANTA: Likitoci su na kukan rashin alawus

“Asali ma, ganin irin yaudarar da shugabannin kwadago su ka yi wa ma’aikata tun da aka dawo mulkin farar hula, ba mu yi mamakin wannan ja-da-baya da aka yi ba.”

Zikirullahi ya ce abin da ya faru a ranar Litinin ya sake fito da yaudarar NLC da TUC na amincewa da zancen kanzon kuregen gwamnati da sunan rage radadin da ake ciki,

A safiyar jiya aka ji cewa shugabannin kungiyoyin NLC ta TUC sun dakatar da maganar shiga yajin aiki bayan sun yi wata doguwar zama da wakilan gwamnatin tarayya.

Festus Keyamo ya ce an janye batun karin farashin wutar lantarki zuwa nan da mako biyu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel