Kungiya ta gano tiriliyan N94.3 da aka karkatar, ta rubutawa Buhari wasika

Kungiya ta gano tiriliyan N94.3 da aka karkatar, ta rubutawa Buhari wasika

- Wata kungiya (ASCAB) ta bayyana cewa an karkatar da makudan kudi har kusan tiriliyan N95 ta hanyar kin sakasu a asusun kasa

- Shugaban kungiyar na wucin gadi, Femi Falana, ya rubuta wasika zuwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin sanar da shi a kan karkatar da kudaden

- ASCAB ta bayyana cewa adadin kudaden za su iya rike Najeriya na tsawon shekaru fiye da takwas a kan kasafin fiye da tiriliyan N10 duk shekara

Wata babbar kungiyar hadakar kungiyoyin da ke rajin tabbatar da daidaituwar al'amura bayan annobar korona (ASCAB) ta bayyana cewa ta bankado tiriliyan N94.3 da aka karkatar da su ta hanyar kin sakasu a asusun kasa.

ASCAB, wacce ta hada kungiyoyin 'yan gwagawarmaya guda 70 ta sanar da hakan ne a cikin wata wasika da ta aikawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.

DUBA WANNAN: Batagari sun kaiwa jami'an kwastam harin kwanton bauna bayan sun kwace shinkafa

A cikin wasikar, mai dauke da sa hannun shugabanta na wucin gadi, Femi Falana (SAN), ASCAB ta shaidawa shugaba Buhari cewa adadin kudaden da ta gano an karkatar, za su iya rike Najeriya na tsawon shekaru fiye da takwas.

Kungiyar ta bayyana cewa Najeriya da dukkan jihohinta su na da isassun kudaden da za su iya biyan bukatun dukkan jama'arsu ba don matsalar 'zurarewar kudin shiga' da ake samu ba.

Kungiya ta gano tiriliyan N9.4 da aka karkatar, ta rubutawa Buhari wasika
Kungiya ta gano tiriliyan N9.4 da aka karkatar, ta rubutawa Buhari wasika
Asali: Facebook

"ASCAB ta yi watsi da batun cewa babu isassun kudaden da za a yi wa jama'a aiki. A yanzu arzikin Najeriya, iya na cikin gida (GDP) da aka auna, ya ninka na shekarar 1998 sau uku, amma kuma darajar albashin yanzu ba ta kai na shekarar 1998 ba.

"An yi karin albashi amma har yanzu wasu jihohi a kalla 8 basu fara nuna alamun za su biya mafi karancin albashi N30,000 da ya zama doka ba tun a watan Yuli na shekarar 2019.

DUBA WANNAN: Rochas ya bayyana ma su jawowa Buhari zagi a wurin 'yan Najeriya

"Gwamnatin tarayya ta na ikirarin cewa ba za ta iya cigaba da biyan tallafin man fetur ba, gwamnatocin jihohi su na kukan cewa ba za su iya biyan mafi karancin albashi ba.

"Sabanin duk wadannan maganganu da gwamnatoci ke fada, ASCAB ta gano cewa gwamnatin tarayya ta na da kudaden da aka karkatar wanda yawansu ya kusa tiriliyan N95.

"Kasafin kudin bana na kasa ya tsaya a tiriliyan N10.8 bayan an yi kwaskwarima, kudin da mu ke magana a kansu, kusan N95tn, sun isa kasafin kasa na shekaru fiye da takwas," a cewar Falana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel