Tun farkon mulkin Buhari, ba a fara da sa'a ba - Oyegun ya bayyana manyan kalubalen APC
- Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa,, ya ce mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zo a hagungunce
- Ya tabbatar da cewa akwai ginshikin cigaba a kasar nan amma tun farkon mulkin babu sa'a
- Ya jajanta yadda tattalin arziki ke karyewa, tsanantar yunwa, rashin aikin yi da kuma ta'addanci a kasar nan
John Oyegun, tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya ce mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance mara sa'a tun farkon shi.
A yayin zantawa da manema labarai a gidansa da ke Benin a ranar Litinin, ya ce ba don salon mulkin ba, da Najeriya bata samu cigaban da ta samu a yanzu ba, The cable ta wallafa.
A yayin jajantawa a kan manyan kalubalen da suka addabi kasa, Oyegun ya ce wadanda ke mulki a yanzu ba su yin kokarin da ya dace kuma hakan ta sa 'yan Najeriya suka sare.
"Al'amura sun yi tsauri. Abinda zan iya cewa shine an gina ginshikin cigabanmu amma kuma mulkin nan babu sa'a," yace.
"Mun samu jarabawoyi masu tarin yawa tun daga farkon mulkin nan kuma duk da haka muna fuskantar cigaba. Babu shakka.
"Akwai yunwa, tattalin arziki baya habaka, rashin aikin yi, ta'addanci da sauransu. Dole ne in bayyana cewa, ina matukar damuwa da yadda komai ke tafiya," yace
KU KARANTA: ICPC ta samo N16 biliyan daga ma'aikatar gona ta tarayya

Asali: Twitter
KU KARANTA: Kanuri: Al'ada, addini, aure, abinci da tsatson babbar kabilar
A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai yuwuwar tarwatsewar Najeriya idan ba'ayi kokarin toshe barakar dake kunno kai ba.
Yace akwai wadanda zasu iya yunkurin hana toshe barakar, amma idan aka jajirce kuma aka dage da addu'a za'a iya cimma gaci.
Osinbajo yayi wannan jan kunnen ne a ranar Lahadi a Abuja a wata tattaunawa da aka yi da shi, saboda shiryawa shagalin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai na Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng