Daga ƙarshe: Kotu ta ci tarar Sanata Abbo N50m saboda cin zarafin wata mace

Daga ƙarshe: Kotu ta ci tarar Sanata Abbo N50m saboda cin zarafin wata mace

- Kotun birnin tarayya ta ci tarar Sanata Elisha Abbo naira miliyan 50 kan cin zarafin wata mata

- An dai kama Abbo da laifin marin matar a wani shagon siyar da kayan jima’i a Abuja

- Abbo dai shine sanata mai wakiltan Adamawa ta arewa a majalisar dattawa

Wata babbar kotun tarayya ta umurci Elisha Abbo, Sanata mai wakiltan Adamawa ta arewa, da ya biya miliyan N50 a matsayin diyya ga Osimibibra Warmate kan cin zarafinta.

A 2019, hukumar yan sanda ta gurfanar da Abbo a gaban wata kotun majistare da ke Zuba, kan wata tuhuma guda da ake masa na cin zarafin Warmate a shagon siyar da kayan jima’i a Abuja.

Duk da hujja na bidiyon lamarin da aka gabatar, Abdullahi Ilelah, alkalin kotun, ya riki takardar babu kara da dan majalisar ya gabatar, sannan ya kori shari’ar.

Daga ƙarshe: Kotu ta ci tarar Sanata Abbo N50m saboda cin zarafin wata mace
Daga ƙarshe: Kotu ta ci tarar Sanata Abbo N50m saboda cin zarafin wata mace Hoto: @thecableng
Source: Twitter

Sai dai kuma, Warmate ta shigar da karar neman yanci a gaban babbar kotun tarayya.

Da yake zartar da hukunci a ranar Litinin, alkalin ya kama Abbo da laifi sannan ya umurce shi da ya biya mai karar miliyan N50, jaridar The Cable ta ruwaito.

Lugard Tare-Otu da Nelson wadanda suka bayyana kansu a matsayin lauyoyin Warmate sun tabbatar da hukuncin kotun a shafin Twitter.

Kun tuna wannan bidiyon sanatan Najeriya da ya mari wata matashiyar mata a shago? Toh gaskiya ta yi halinta a yau inda kotu ta ci tarar sanatan N50M. Ina farin cikin wakiltan wannan matashiya a wannan kara,” in ji Nelson.

A wani labarin, ranar Litinin, kwararru a Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci Nigeria da ta saki mawakin da aka yankewa hukuncin kisa saboda zarginsa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

A watan da ya gabata ne wata kotun shari'a a Kano, ta yankewa Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa, bayan da ya yi wakar batanci ga Musulunci da Annabi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel