Labari mai zafi: Kungiyar kwadago ta cin ma yarjejeniya da Gwamnati

Labari mai zafi: Kungiyar kwadago ta cin ma yarjejeniya da Gwamnati

- Kungiyoyin NLC ta TUC sun dakatar da maganar shiga yajin aiki a Yau Litinin

- Hakan na zuwa ne bayan zaman da ‘yan kwadagon su ka yi a gwamnati a jiya

- An janye batun karin farashin wuta zuwa nan da mako biyu inji Festus Keyamo

Kungiyar kwadagon Najeriya da takawararta ta ‘yan kasuwa, sun janye yunkurin tafiya gagarumin yajin aiki a yau Litinin, 28 ga watan Satumba, 2020.

NLC ta TUC sun dakatar da maganar yajin aikin ne bayan sun yi yarjejeniya da gwamnatin tarayya a wani zama da su ka fara cikin daren ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce an fara wannan taro ne tun da kimanin karfe 8:30 na daren jiya, an kuma kai ga cin ma yarjejeniya da karfe 2:50 na safiyar yau dinnan.

Bayan tsawon lokaci ana tattaunawa kan batutuwan da kungiyoyin kwadagon su ka kawo, gwamnatin tarayya ta dakatar da karin kudin wuta na mako biyu.

KU KARANTA: Kotu ta hana 'Yan kwadago tafiya yajin aiki

Ministan kwadago na kasa, Sanata Chris Ngige ya karanto takardar matsayar da aka cinma tsakanin wakilan ma’aikata da kuma gwamatin tarayya.

Shugabannin TUC da kungiyar NLC; Quadri Olaleye da Ayuba Wabba su na cikin wadanda su ka sa hannu a madadin kungiyoyin ma’aikatan Najeriya.

A bangaren gwamnati kuwa, wadanda su ka sa hannu sun hada da Ministocin kwadago, da yada labarai, Chris Ngige, Festus Keyamo da Lai Mohammed.

Haka zalika karamin Ministan harkokin man fetur, Timipre Silva, da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sun rattaba hannu a wannan yarjejeniya.

KU KARANTA: Abin da zai hana mu zuwa yajin-aiki - NLC

Labari mai zafi: Kungiyar kwadago ta cin ma yarjejeniya da Gwamnati
'Yan kwadagon Najeriya Hoto: Punch
Source: Twitter

Festus Keyamo ya tabbatar da cewa babu batun janye tsarin kudin man fetur, amma an dakatar da karin kudin wutar lantarki har sai nan da makonni biyu.

A dalilin zaman na dazu, an kafa kwamitoci daga ma’aikatun gwamnati da kuma bangarorin ‘yan kwadago domin a cika wadannan alkawaru da aka dauka.

A jiya kun ji cewa Gwamnatin tarayya za ta gana da kwadago da karfe 7:00 na yamma saboda yunƙurin shiga yajin aiki da ma'aikata ke yi a fadin Najeriya.

Gwamnati ta yi kokarin hana tafiya jayin aikin da aka shirya kan karin farashin wuta da mai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel