Adana karfinka domin amfanin wata rana - Matawalle ga matashin da zai yi masa tattaki

Adana karfinka domin amfanin wata rana - Matawalle ga matashin da zai yi masa tattaki

- Gwamnan jihar Zamfara ya dakatar da matashin dake tattaki daga Kaduna zuwa Zamfara don nuna masa kauna

- Gwamnan ya shawarci matashin da yayi amfani da karfinsa wurin amfanar al'umma baki daya

- Matashin ya dage lallai sai ya karasa tattakin sa koda yan fashi zasu tareshi a hanya

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya dakatar da matashin dake tattaki daga Zamfara zuwa Kaduna saboda nuna masa soyayya.

Ku tuna, a ranar Alhamis, wani matashi mai suna Musa Umar, ya fara tattaki tun daga kauyensu, wato karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna, zuwa jihar Zamfara saboda nuna wa gwamnan jihar Zamfara kauna.

A ranar juma'a, 26 ga watan Satumba, Gwamna Matawalle ya mika sakon godiyarsa ga matashin amma ya dakatar dashi daga tafiyar mai cike da hadari.

Gwamnan ya wallafa hakan ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter inda ya ce, "Nagode kwarai da nuna soyayyar da matashin nan mai tattaki zuwa jihata saboda nuna min soyayya yakeyi.

"Amma a matsayina na uba, ina mai shawartar matasa da su kiyayi tafiye-tafiye masu hadari irin wannan, nagode amma ya dakatar da tattakin sa, ya kuma adana karfinsa wurin yin wani abu da zai amfani al'umma." Inji Gwamnan.

Matashin ya cigaba da tafiyar, har ya mayar wa da gwamnan martani, ya ce shifa yana nan akan bakan sa, kuma koda zai hadu da yan fashi, sai ya karasa jihar Zamfara saboda nuna kauna ga gwamnan.

Ya mayar da martanin a kasan rubutun gwamnan inda yace, "nifa bazan gushe ba, ko da kuwa yan fashi zasu tare ni a hanya,har sai nazo gareka" a cewar matashin.

KU KARANTA: Bidiyon karamar yarinya tana bai wa iyayenta shawara a kan aure ya janyo cece-kuce

Adana karfinka domin amfanin wata rana - Matawalle ga matashin da zai yi masa tattaki
Adana karfinka domin amfanin wata rana - Matawalle ga matashin da zai yi masa tattaki. Hoto daga Musa Umar Giwa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Babban kwamandan Boko Haram da matansa 4 sun mika kansu ga sojoji a Borno

A wani labari na daban, bidiyon wata karamar yarinya ya bar jama'a da dama baki bude sakamakon hazaka da kaifin basirarta wurin nuna kaunar iyayenta.

A bidiyon mai tsayin minti uku, an ga yarinyar tana bai wa iyayenta shawarwarin zamantakewar aure. Tiana ta bada wannan shawarar ne domin taimaka wa iyayenta wadanda suka rabu kuma kullum suke fada.

Abinda yarinyar karama take bukata shine iyayenta su zama abokan juna, su daina fada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel