Kalli sabon hoton biloniyan Najeriya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina da yaransa mata su 16

Kalli sabon hoton biloniyan Najeriya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina da yaransa mata su 16

- Wani sabon hoto na iyalan biloniya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ya bayyana

- An gano shahararren dan kasuwar zaune a tsakiyar yaran nasa su 16 wanda dukkansu mata ne

- Sarina dai shine shugaban rukunin kamfanonin Azman, wato kamfanin sufuri na Azman da na hada-hadar man fetur da gas da kuma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama

Kamar yadda kuka sani, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, ya kasance shahararren dan kasuwa Najeriya kuma yana cikin sahun farko na biloniya a kasar.

Har ila yau Sarina ya kasance shugaban rukunin kamfanonin Azman, wato kamfanin sufuri na Azman da na hada-hadar man fetur da gas da kuma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Azman.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sake kashe wani babban kanal din soji a Katsina

Kalli sabon hoton biloniyan Najeriya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina da yaransa mata su 16
Kalli sabon hoton biloniyan Najeriya, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina da yaransa mata su 16 Hoto: arewa_heritage
Source: Instagram

Baya ga arziki na kudi da Allah ya azurta dan kasuwar da shi, ya kuma azurta shi da haihuwar yaya da yawa.

A bisa ga wani hoto shafin Instagram na ‘Arewa Heritage’ya wallafa, an gano mai rukunin kamfanonin na Azman tare da ahlinsa su goma sha shida, wadanda aka bayyana a matsayin yaransa mata.

KU KARANTA KUMA: Sultan Hassanal Bolkiah: Hamshakin mai arzikin da ya mallaki Rolls Royce 500, N7m kudin askinsa

A jikin hoton an wallafa rubutu kamar haka: “Ahlin Azman da mahaifinsu...Babban tawaga ke garemu.”

A wani labari na daban, Marigayi Alhaji Mai Deribe babu shakka yana daya daga cikin hamshakan masu kudi a Najeriya a shekarun 1980.

Ya gina gida wanda aka yi shi da ruwan zinari sannan ya mallaki wani jirgin sama kirar Gulfstream G550.

Kamar yadda Northeast Reporters suka wallafa, yana daya daga cikin mutane 12 da suka taba mallakar irin wannan jirgin saman a fadin duniya.

Gidansa, wanda ake kira da Gidan Deribe, ya ja hankulan jama'a masu tarin yawa a duniya.

Ba abun mamaki bane ganin yadda ya dinga saukar manyan mutane a duniya kamar Yarima Charles da matarsa, marigayiya Gimbiya Diana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel