Jami'an Sojin kasa da kasa MNJTF sun ceto mutane 12 da Boko Haram suka sace

Jami'an Sojin kasa da kasa MNJTF sun ceto mutane 12 da Boko Haram suka sace

- Gabanin harin da aka kaiwa tawagar gwamna Zulum, Soji sun ceci mata da yara daga hannun Boko Haram

- Gwamna Zulum ya kai ziyara Baga ranar Juma'a tare da manyan mukurrabansa

Jami'an Sojojin kasa da kasa MNJTF sun ceto mutane 12 da yan ta'addan Boko Haram da ISWAP suka sace.

Sojojin sun kaiwa yan ta'addan farmaki ne kuma suka ceci wadanda aka sace a ranar Alhamis.

Shugaban yada labarai na rudunar Sojin MNJTF, Kanal Muhammad Dole a ranar Asabar ya ce, "mun cigaba da ganawa yan ta'addan Boko Haram/ISWAP azaba a yankin tafkin Chadi.

"Bayan samun labarin cewa yan ta'addan na shirin canza inda suke boye, dakarun Sakta 2 (Chadi) na rundunar kasa da kasa sun afkawa yan ta'addan a kusa da Barkalam."

"Yayin artabun, jiragen ruwa uku sun kife kuma hakan yayi sanadiyar mutuwa da damke yan ta'addan, yayinda sauran suka jiggata."

"Sakamakon harin, an samu nasarar ceton mutane 12 daga hannun yan Boko Haram/ISWAP. Mutanen da aka ceto sun hada da namiji daya, mata uku da yara takwas."

"Hedkwatar MNJTF ta yi amfani da jirgi mai saukar angulu wajen kai su N'Dajemana daga Baga Sola."

KU KARANTA: Adadin mutanen da yan Boko Haram suka kashe a harin da su kaiwa gwamna Zulum

Jami'an Sojin kasa da kasa MNJTF sun ceto mutane 12 da Boko Haram suka sace
Jami'an Sojin kasa da kasa MNJTF sun ceto mutane 12 da Boko Haram suka sace
Source: Twitter

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya yi Allah wadai ta harin da aka kai wa tawagar gwamnan Borno, Babagana Zulum da ya yi sanadin rasuwar jami'an tsaro da wasu 'yan civilian JTF.

An tabbatar da mutuwar a kalla jami'an tsaro 11 a harin na ranar Juma'a, wanda shine na biyu da ake kai wa tawagar Zulum a jiharsa.

A sanarwar da ta fito daga kakakin shugaban kasa Garba Shehu, shugaban kasar ya ce harin a aka kai a hanyar Maiduguri - Baga wani mataki ne na hana mayar da 'yan gudun hijira gidajensu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel