Zan mara wa Tinubu idan ya fito takarar shugaban kasa - Sanata Buhari

Zan mara wa Tinubu idan ya fito takarar shugaban kasa - Sanata Buhari

- Sanata Abdulfatai Buhari, dan majalisa mai wakiltar Oyo ta Arewa ya ce zai mara wa Bola Tinubu baya idan ya fito takarar shugabancin kasa a 2023

- Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin zantawa da wani dan jarida mai suna Edmund Obilo a ranar Alhamis

- Sanata Buhari ya kuma bayyana cewa ba gaskiya bane rade-radin da ake yi na cewa Gwamna Fayemi na Ekiti na yi wa Tinubu zagon kasa

Dan majalisa mai wakiltar Oyo ta Arewa, Sanata Abdulfatai Buhari ya ce zai goyi bayan jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu idan ya nuna sha'awar fitowa takarar shugabancin kasa a Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin hirar da ya yi da wani dan jarida, Edmund Obilo a ranar Alhamis kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Zan mara wa Tinubu idan ya fito takarar shugaban kasa - Sanata Buhari
Zan mara wa Tinubu idan ya fito takarar shugaban kasa - Sanata Buhari. Hoto daga @PremiumTimesng
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Mayakan ISWAP sun afka wa tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar Borno

Da aka masa tambaya shin ko da gaske ne Gwamna Fayemi Kayode na jihar Ekiti na yi wa Tinubu zagon kasa, Buhari ya ce hakan ba gaskiya bane.

Ya amsa da cewa, "A'a. Ni Tinubu ne. Ni ba Fayemi bane kuma ba zan zaune inda wani ke yi wa Tinubu zagon kasa ba ba. Ina goyon bayan Tinubu.

Da ya ke amsa tambayar da aka masa na sanin ko Tinubu zai yi takarar shugaban kasa, Buhari ya ce, "Idan yana son zama shugaban kasa, Zan mara masa baya. Zan yi masa kamfen."

KU KARANTA: Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

A kan batun rikicin jam'iyyar APC a jihar ta Oyo, dan majalisar ya ce rasa kujerer gwamna da APC ta yi a jihar ne ya janyo rikicin.

Ya kuma ce tsohon gwamnan jihar Oyo, Adebayo Alao-Akala ne jagoran jam'iyyar a jihar.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel