Mutum 30 sun mutu a harin da ISWAP ta kai wa tawagar gwamnan Borno

Mutum 30 sun mutu a harin da ISWAP ta kai wa tawagar gwamnan Borno

- Wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne sun kai wa tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar Borno hari safiyar yau Juma'a

- Rahotanni daga majiyar tsaro sun ce mutum 30 ne suka rasu sakamakon hari, cikinsu akwai 'yan sanda, sojoji, farar hula da 'yan JTF

- 'Yan ta'addan sun kuma kwace motocci masu bindiga na 'yan sanda, sojoji da motoccin zirga-zrga na gwamnatin jihar Borno

Mayakan ISWAP sun afka wa tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar Borno
Mayakan ISWAP sun afka wa tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar Borno. Getty images
Source: Getty Images

DUBA WANNAN: Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

'Yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne a ranar Juma'a sun kai wa tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar Borno hari inda suka kashe mutum 30 ciki har da jami'an tsaro 17 a hanyarsu ta zuwa Bama a Borno a cewar majiyoyi.

Mutane da dama kuma sun samu rauni sakamakon harin da 'yan ta'addan suka kai wa tawagar.

Wani majiya daga hukumomin tsaro ta ce abinda ya faru sakamakon harin lamari ne mai tayar da hankali.

"An tabbatar da mutuwar 'yan sanda 12, sojoji 5, farar hula 13, mambobin JTF hudu. Yan ta'addan sun kuma kwace motar 'yan sanda mai bindiga daya, motan sojoji mai bindiga daya da motoccin daukan kaya shida mallakar gwamnatin jihar Borno," a cewar majiyar tsaron.

KU KARANTA: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

"An dakile harin nan take amma muna zargin ISWAP ce ta kai wa tawagar gwamnatin jihar hari a hanyarta na zuwa Baga don aikin mayar da 'yan gudun hijira," a cewar majiyar tsaron.

Wata majiyar daban ta ce harin ya faru ne wasu kilomita kadan daga hedkwatan MJTF da ke Baga, inda ya kara da cewa an kai wadanda suka yi rauni babban asibitin Monguno.

A watan Yulin wannan shekarar, an taba kai wa Gwamna Zulum hari tare da tawagarsa a kusa da wannan wurin a hanyarsa na dawowa daga Baga.

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel