Hadiza El-Rufai na son mace ta gaji Sarkin Zazzau Shehu Idris

Hadiza El-Rufai na son mace ta gaji Sarkin Zazzau Shehu Idris

- Hadiza Isma El-Rufai, Uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ta ce tana son ganin an nada mace sarki tamkar yadda aka taba samu a zamanin sarauniya Amina

- Hadiza El-Rufai ta bayyana hakan ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Juma'a 25 ga watan Satumba a yayin da ake jirar masu zaben sarki su mika wa gwamna sunaye

- Kawo yanzu dai gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai bai amsa wa Uwargidansa tambayar da tayi ba na cewa ko hakan na iya samuwa

KU KARANTA: APC ta dakatar da hadimin Buhari, surukin Tinubu da wasu mutane takwas

Hadiza El-Rufai na son mace ta maye gurbin Sarkin Zazzau Shehu Idris
Hadiza Isma El-Rufai. Hoto daga @hadizel
Asali: Twitter

A yayin da al'umma ke jiran masu zaben sarki a masarautar Zazzau su mika wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai sunayen wadanda suka tantance domin ya zaba sabon sarki, uwargidansa Hadiza Isma El-Rufai ta roke shi ya maye gurbin sarkin da mace.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Tuwita @hadizel, ta ce don tabbatar da daidaito tsakanin jinsin maza da mata, ko akwai yiwuwar a sake samun Sarauniya a Zazzau kamar Amina?

DUBA WANNAN: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Kawo yanzu dai gwamnan na jihar Kaduna bai bata amsa ba amma a jiya Alhamis 24 ga watan Satumba ya ce ya mayar da hankali yana karanta wani littafi da aka dade da wallafawa kan nadin sarauta a masarautar da wani bature ya wallafa.

Mutane da dama sun ta tofa albarkacin bakinsu a kan batun bayan sakon da Hadiza El-Rufai ta wallafa, wasu sun goyi bayan ta a yayin da wasu ke ganin abinda ta ke nema zai yi wahalar samu a wannan zamanin.

A wani labarin daban. Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel