Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari

- An daura auren Bashir Ahmad da sahibarsa Naeemah Bindawa, a ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba, 2020

- An daura auren ne a babban Masallacin Juma'a na G.R.A, jihar Katsina, inda dandazon mutane suka taru don shaida wannan aure

- Bashir Abdullahi El-Bash, aminin angon, ya wallafa zafafan hotunan auren hadimin shugaban kasar ta fuskar kafofin sada zumunta na zamani

A ranar Juma'a, Allah ya kaddara, aka daura auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta, tare da amaryarsa, Naeemah.

An daura auren Bashir da Naeemah a babban Masallacin G.R.A, jihar Katsina, inda dubunnan mutane suka taru don shaida wannan aure.

Kamar yadda kuka sani burin kowasu masoya da suka tsinci kansu a cikin shau’kin so, shine ganin sun mallaki junansu ta hanyar kulla aure a tsakaninsu.

KARANTA WANNAN: Sabbin mutane 125 sun kamu da cutar COVID-19, jimilla 57,849

Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari
Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari
Asali: Twitter

Ko shakka babu hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya tsunduma sosai a cikin kaunar burin ransa, Naema.

Bashir ya nuna farin ciki a yayinda yake shirin fita daga sahun gwauraye, domin ko a ranar Alhamis, 24 ga watan Satumba, sai da ya wallafa magana mai ratsa zuciya akai.

KARANTA WANNAN: Wannan shine shan shayina na karshe a matsayin gwauro - Bashir Ahmad

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mai ba Shugaban kasar shawara ya bayyana cewa a ranar Alhamis, 24 ga watan Satumba, ya sha shayinsa na karshe a matsayin gwauro.

Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari
Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari
Asali: Twitter

Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari
Hotunan Naema, amaryar Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari - Bashir Abdullahi El-Bash
Asali: Facebook

Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad tare da amaryarsa Naema - Bashir Abdullahi El-Bash

A wani labarin, Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewa sabbin mutane 125 ne suka kamu da cutar COVID-19 a kasar, inda aka samu jimillar mutane 57,849 da ke dauke da ita.

Hukumar NCDC ta sanar da hakan a shafinta na Twitter @@NCDCgov a daren ranar Alhamis.

Hukumar ta kuma sanar da cewa, mutane 49,098 suka warke sarai daga cutar kuma har an sallamesu daga asibiti, yayin da mutane 1,102 suka mutu sakamakon cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel