Na yi farin cikin shan kaye a zaben gwamnan Oyo a 2019 - Dan takarar APC

Na yi farin cikin shan kaye a zaben gwamnan Oyo a 2019 - Dan takarar APC

- Bayo Adelabu, dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a zaben 2019 a jihar Oyo ya ce ya yi farin cikin i fadi zabe da ya yi a 2019

- A cewar Adelabu, shan kayen da ya yi ya bashi damar kara hikima kan yadda al'amurra ke gudana a jihar da kusantar talakawa da shugabannin jam'iyya

- Mista Adelabu ya ce ya yi imanin zai fi dacewa ya zama gwamna a 2023 inda ya soki irin kamun ludayin gwamnatin Gwamna Makinde na PDP mai mulki a jihar

Na yi farin cikin shan kaye a zaben gwamnan Oyo a 2019 - Dan takarar APC
Bayo Adelabu. Hoto daga @Inisideoyo
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2019 a jihar Oyo, Bayo Adelabu ya ce ya yi farin cikin shan kaye da ya yi a zaben da ya gabata.

Ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Ibadan, babban binrin jihar Oyo a ranar Alhamis a wurin taron cin abinci don murnar cikarsa shekaru 50 a duniya.

Tsohon mataimakin babban bankin na kasa, CBN, ya ce rashin yin nasara a zaben ya bashi damar sake yin nazarin yadda jam'iyyar ta APC da masu son cigaba ke yin ayyuka a jihar.

KU KARANTA: APC ta dakatar da hadimin Buhari, surukin Tinubu da wasu mutane takwas

"Na kara hikima a siyasance, na kara kusantar shugabannin jam'iyya da talakawa. Yanzu na san yadda zan rika mu'amulla da masu kishin jam'iyya. Zai fi dacewa in zama gwamna a 2023 a maimakon 2019.

"Yanzu zan rika shiga siyasa a dama da ni. Ba zan taba dena sha'awari shiga takara ba. Na yi imanin zan kawar da PDP idan mun hada kai a 2023. Bayan taron da muka yi a baya bayan nan, babu wanda zai iya kayar da APC a 2023," ya ce.

Mista Adelabu ya kuma soki gwamnatin PDP na Seyi Makinde mai mulki yanzu a jihar. Ya ce gwamnatin na yanzu ba ta da alkibla.

"Bisa ga dukkan alamu zan kayar da Makinde. Bai shi da basira. Har yanzu watanni 16 bayan zabensa bai cika alkawurran da ya yi wa mutane ba. Idan aka yi la'akari da irin mutanen da suka dawo APC, babu jam'iyyar da za ta iya taka wa APC birki," in ji shi.

A wani labarin, Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya amince da nadin sabbin mataimakansa na musamman na bangaren dandalin sada zumunta 30 hakan ya kawo adadin hadiman da gwamnan ke da su zuwa 672.

A baya, Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya nada hadimai 642 da suka hada da manyan hadimai na musamman da jami'an tuntuba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel