Gwamna Borno Babagana Zulum ya lashe kyautar gwarzon shugaba ta Zik

Gwamna Borno Babagana Zulum ya lashe kyautar gwarzon shugaba ta Zik

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya lashe kyautar Zik ta shekarar 2019 a rukuncin shugabanni

- Cibiyar bincike kan tsare-tsare, PPRAC, ce ke bada kyaututukan da mutanen da suka nuna bajinta a bangarorin ayyukansu a duk shekara

- A jawabin da ya yi yayin sanar da kyautan, Farfesa Pat Utomi ya ce nasarori da jajircewa wurin aiki irin na Zulum ne yasa ya samu kyautar cikin sauran gwamnonin kasar

DUBA WANNAN: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Borno: Zulum ya lashe lashe kyautar Zik na Shugabanci na 2019
Borno: Zulum ya lashe lashe kyautar Zik na Shugabanci na 2019. Hoto @GuardianNigeria
Source: Twitter

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Utomi ya bayyana Zulum a matsayin gwamna mai hangen nesa da ya zama cikin shugabanni a Najeriya wadanda suka samu nasarori masu yawa cikin kankanin lokaci.

Farfesa Utomi ya yi wannan jawabin ne ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti na zoom kuma ya yi magana ne a madadin kwamitin masu bada shawarwari na Cibiyar bincike kan tsare-tsare, PPRAC, wacce Farfesa Jubril Aminu, tsohon minista kuma sanata ke shugabanci.

KU KARANTA: Gwamnati ta fitar da $1.96bn don ginin layin dogo daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar

Emeka Obasi ne sakataren kwamitin yayin da mambobinta sun hada da Farfesa George Obiozor, Cif Marc Obara, Cif Tola Adeniyi, Alhaji Abdulazeez Udeh da Pat Utomi.

Sauran wadanda suka lashe kyaututukan a wasu rukunonin sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, SGF Boss Mustapha, Dakta Stella Okolli, Farfesa Umar Danbatta da Kennedy Nduka a cewar Utomi.

A rukunin shugabanci na gari, cikin gwamnonin Najeriya 36, Farfesa Utomi ya ambaci Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta da Farfesa Zulum na jihar Borno.

Amma Utomi ya dauki lokaci mai tsawo yana jawabin yabo kan Zulum da yace 'yan Najeriya daga bangarori daban-daban na yabonsa.

Zulum shine gwamna na farko da ya taba lashe kyautar a wa'adin mulkinsa na farko.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel