Babban kwamandan Boko Haram da matansa 4 sun mika kansu ga sojoji a Borno

Babban kwamandan Boko Haram da matansa 4 sun mika kansu ga sojoji a Borno

- Wani babban kwamanda a gagarumar kungiyar ta'addanci Boko Haram, ya mika kansa ga dakarun sojin Najeriya

- A tare da babban kwamandan da ya mika wuyan, akwai matansa hudu da suka mika kai tare

- Kamar yadda Manjo Janar John Enenche ya sanar, ya ce wannan nasarar an sameta sakamakon aiki tukuru na rundunar

Babban kwamandan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, tare da matansa hudu, sun mika kansu ga rundunar sojin kasa ta Najeriya, Channels TV ta wallafa.

Hakazalika, an halaka 'yan bindiga bakwai tare da ceto wasu mutum 8 da aka yi garkuwa da su a Fankama da Sabon Layi da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Kastina.

Wannan na kunshe a wani jawabi na shugaban fannin yada labarai, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana yayin jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a Abuja.

Duk da Enenche bai bada gamsasshen bayani a kan kwamandan da ya mika kansa ba, ya ce wannan nasarar ta samu ne bayan kokari da jajircewar da dakarun suka bayyana.

"A yankin arewa maso gabas, rundunar Operation Lafiya Dole ta aiwatar da jerin samame ta jiragen yaki da kuma kasa, inda ta dinga bankado maboyar 'yan ta'adda a jihohin Borno, Yobe, Taraba da ADamawa.

"Hakazalika, babban kwamandan da kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ke ji da shi, tare da matansa hudu sun mika kansu ga dakarun," yace.

KU KARANTA: Karin farashin wutar lantarki: Karuwai suna shirin fadawa yajin aiki

Babban kwamandan Boko Haram da matansa 4 sun mika kansu ga sojoji a Borno
Babban kwamandan Boko Haram da matansa 4 sun mika kansu ga sojoji a Borno. Hoto daga @ChannelsTv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan shan mugun kaye, Ize-Iyamu na jam'iyyar APC ya aike wa Obaseki muhimmin sako

A wani labari na daban, sama da mutane 20 da aka yi garkuwa da su, da suka hada da mata 11 da kananun yaran da ba a san iyakarsu ba, suka samu ceto daga hannun 'yan bindiga, a sassa daban na jihar Katsina.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a garin Fankama da Sabon Layi, karamar hukumar Faskari, mutane 8 ne rundunar soji ta ceto su daga 'yan bindigar, bayan samun rahotanni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel