Badakalar N800m: An tsare shugaban jam'iyyar APC na jihar Niger a gidan gyaran hali

Badakalar N800m: An tsare shugaban jam'iyyar APC na jihar Niger a gidan gyaran hali

- Kotu ta bada umurnin a ajiye mata shugaban jam'iyyar APC na jihar Niger da mataimakinsa a gidan gyaran hali

- Ana tuhumar shugaban na APC Jibrin Imam da Sakataren jam'iyyar Shafi Abdulsalam ne da laifin bannatar da N800m na jam'iyyar

- Lauya mai kare wadanda ake zargin ya nemi a bada belin su amma alƙalin kotun ya ce a ajiye su zuwa ranar Juma'a

An aike da shugaban jam'iyyar APC na jihar Niger, Jibrin Imam da Sakataren jam'iyyar Shaffi Abdulsalam gidan gyaran hali a ranar Laraba a Minna kafin su cika ka'idar beli.

An gurfanar da mutanen biyu ne a gaban alƙalin kotun Majistare, Nasiru Mu'azu kan tuhumar su da laifuka uku masu alaka da hadin baki, cin amana da bannatar da kuɗi.

Badakalar N800m: An tsare shugaban jam'iyyar APC na jihar Niger a gidan gyaran hali
Badakalar N800m: An tsare shugaban jam'iyyar APC na jihar Niger a gidan gyaran hali. Hoto daga @GuardianNigeria
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Borno: An sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Mai shigar da ƙarar, ASP Ahmed Saidu ya ce Imam da Shaffi da wasu biyu da ake nema sun hada baki sun bannantar da Naira miliyan 800 mallakar jam'iyyar APC na jihar.

Mai shigar da ƙarar ya yi iƙirarin cewa wadanda ake zargin sun "kuma bannatar da kudaden APC na jihar Niger sannan suna ta amfani da kuɗin jam'iyya don yin hidimomin gabansu."

Ya ƙara da cewa wadanda ake zargin sun fitar da kudaden ba bisa ka'ida ba kuma ba su bayyana abinda suka yi da kudin ba.

Ɗan sanda mai shigar da ƙarar ya yi iƙirarin jami'in walwala na jam'iyyar, Alhaji Muka Fasasi ya amsa cewa ya karbi Naira miliyan 4.8 daga wurin mambobin majalisar jihar ya raba wa mutane.

KU KARANTA: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Mai shigar da ƙarar ya ce bai amince a bada su beli ba domin har yanzu akwai biyu daga cikinsu da ba a kamo su ba.

Amma, lauyan wadanda ake zargin, Isah Suleiman ya roki kotun ta bada belin su.

Alƙalin kotun bai yanke hukunci kan neman belin ba har zuwa ranar Juma'a ya kuma umurci a bawa wadanda ake zargin masauki a gidan gyaran hali.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel