Bidiyon karamar yarinya tana bai wa iyayenta shawara a kan aure ya janyo cece-kuce

Bidiyon karamar yarinya tana bai wa iyayenta shawara a kan aure ya janyo cece-kuce

- Mahaifiyar Tiana, Cherish Sherry ce ta fara wallafa bidiyon diyarta wanda ya karade kafafen sada zumunta

- Jama'a masu tarin yawa sun dinga yaba wa hazakarta da kuma ilimin yarinyar wurin shawo kan matsaloli

- Daga tsokacin jama'a, an ji yadda suke jinjina mata a kan kaifin tunani da basirarta wacce ta fi wasu manyan

Bidiyon wata karamar yarinya ya bar jama'a da dama baki bude sakamakon hazaka da kaifin basirarta wurin nuna kaunar iyayenta.

A bidiyon mai tsayin minti uku, an ga yarinyar tana bai wa iyayenta shawarwarin zamantakewar aure.

Tiana ta bada wannan shawarar ne domin taimaka wa iyayenta wadanda suka rabu kuma kullum suke fada.

Abinda yarinyar karama take bukata shine iyayenta su zama abokan juna, su daina fada.

"Mama, kin shirya zama kawarsa? Ina son komai ya lafa, kin ji?" ta tambaya mahaifiyarta.

KU KARANTA: Yadda ubangidana yake daureni yana lalata da ni, yana bani magani da giya don kada in dauka ciki - 'Yar aiki

Bidiyon karamar yarinya tana bai wa iyayenta shawara a kan aure ya janyo cece-kuce
Bidiyon karamar yarinya tana bai wa iyayenta shawara a kan aure ya janyo cece-kuce. Hoto daga Junkin Media
Source: UGC

Kamar yadda hazikar yarinyar tace, abinda take so shine ganin farin ciki a tattare da su ba fada kullum ba.

"Ina kokarin ganin kun zama nagari. Bana son ganin ki da mahaifina kuna fada, ba zan iya maye gurbinku da kowa ba. Ku sasanta junanku," tace.

Tiana ta yi kira ga iyayenta da su ajiye dukkan makaman rikicinsu, sannan su rungumi zaman lafiya a tsakaninsu.

KU KARANTA: Bayan shan mugun kaye, Ize-Iyamu na jam'iyyar APC ya aike wa Obaseki muhimmin sako

A wani labari na daban, Kensmith Rechiel wani yaro ne mai cike da abin mamaki wanda ya kirkiri abubuwa da dama.

Ya kirkiri babur, jirgin sama mai daukar mutum daya, jirgin kasa mai daukar mutane biyu har da mota mai amfani da remote duk kafin ya cika shekaru 18 da haihuwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel