An bayyana hamshakin mai kudi dan Najeriya a cikin mutane 100 da suka fi kowa alfarma a duniya

An bayyana hamshakin mai kudi dan Najeriya a cikin mutane 100 da suka fi kowa alfarma a duniya

- Fitaccen dan kasuwa dan Najeriya Tony Elumelu ya shiga cikin jerin mutum 100 da suka fi kowa alfarma a duniya

- Mashahurin dan kasuwarnan mai taimako ya shiga cikin mutane 4 da sukafi kowa kudi a Afirka a shekarar 2020

- Elumelu ya samu sanayya ne akan taimakonsa da tallafawa yan kasuwa masu karamin karfi

Jaridar Times ta bayyana fitaccen biloniya kuma babban dan kasuwa Tony Elumelu a matsayin mutumin da ya shiga cikin jerin mutane 100 da suka fi kowa alfarma a duniya.

Times suna amfani da ayyuka, taimako, kirkire-kirkire da kuma nasarorin attajirai wurin kirga masu alfarma a duniya.

Dan kasuwar yayi fice sakamakon bunkasa tattalin arzikin masu karamin karfi, da kuma taimaka musu basu jari da tallafawa sana'o'insu.

Elumelu nada hannayen jari a bankuna, wuraren shakatawa, kamfanin wutar lantarki da kuma asibitoci.

An bayyana hamshakin mai kudi dan Najeriya a cikin mutane 100 da suka fi kowa alfarma a duniya
Tony Elumelu | Photo credit: Premium Times
Source: UGC

Dan kasuwar yayi amfani da shafinsa na sada zumuntar zamani na Twitter wurin bayyana yadda ya samu damar shiga cikin wadannan jerin mutane na duniya a shekarar 2020 duk kuwa da cewa shekarar tazo da kalubale iri-iri.

Elumelu ya rubuta a shafin nasa cewa: "A 2010, mun kaddamar da gidauniyar Tony Elumelu ga kungiyar yan kasuwar Champion, mun yunkura wurin kara wa yan kasuwar Afirka karfi."

"A Afirka ne zakaga inda maza da mata masu kananun shekaru ke kokarin bunkasa tattalin arziki, da kirkiro sana'o'i da kuma fuskatar barakar da ta zagaye Afirka."

Ya kara da cewa, "Na lura Afirka cike take da masu neman na kansu. Kuma yan kasuwar Afirka suna kokarin bunkasa tattalin arzikin ta, da kuma neman cigaban nahiyar.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin cigaba da kiran Sallah a wani Masallaci da aka hana a kasar Jamus

Banda Elumelu, wani likitan kwakwalwa dake Legas mai suna Dr Tunji Funsho, da kuma Tomi Adeyemi, suma sun samu shiga cikin jerin mutanen.

Dr Funsho ne likitan farko da ya fara bada gudunmawa akan yawon yin riga-kafin cutar Polio a Afirika.

Likitan yace "nayi farin ciki da har TIME suka lura da tawa gudunmawar wurin yaki da cutar Polio mai cutar da sashin jikin yara. Cutar da ta nakasa yara 75,000 a Afirka cikin shekara daya"

KU KARANTA: Yadda wata budurwa 'yar Najeriya ta samu wata gagarumar kyauta daga wajen mai kudin duniya Bill Gates

Yan Najeriya sunata zama abubuwan alfahari a wurare daban-daban na duniya.

Yanzu haka, tauraruwar Kikelomo Lawal wacce aka fi sani da "Kike" ke haskawa, wadda mai girma mataimakin shugaban kasa kuma shugaban lauyoyi na bankin 'yan kasuwa na kasar Canada (CIBC) ya bata babban matsayi.

Kafin samun wannan matsayin, ita ce shugabar lauyoyin Ombudsman kuma sakatariyar Interac Corp na tsawon shekaru 12 da watanni 8.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel