Dauke da tsohon ciki matar aure tayi kundunbala ta fada cikin ruwa domin ceto mijinta da kifi ke shirin cinyewa

Dauke da tsohon ciki matar aure tayi kundunbala ta fada cikin ruwa domin ceto mijinta da kifi ke shirin cinyewa

- Wata mata mai juna biyu ta samu nasarar ceton mijinta daga bakin katon kifi a Florida

- A ranar 20 ga watan Satumba ne kifin ya kaiwa wani mutumi dake cikin jirgin ruwa hari

- Sakamakon ciwu kan da yaji, yanzu haka yana asibiti rai a hannun Allah

Wata mata mai dauke da juna biyu ta fada cikin ruwa don ceton rayuwar mijinta lokacin da wani katon kifi ya kai mishi farmaki a Florida.

A ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba wani kifi ya kaiwa wani mutumi mai suan Andrew Eddy, mai shekaru 30 da haihuwa farmaki, yayin da yake cikin jirgin ruwansa a yankin Sombrero a Florida.

A yadda rahotonni suka nuna, katon kifin ya ciji kafadar mutumin ne, sakamakon haka ya sanya take a wajen jirgin ya kife cikin ruwa.

Dauke da tsohon ciki matar aure tayi kundunbala ta fada cikin ruwa domin ceto mijinta da kifi ke shirin cinyewa
Matar aure tayi kundunbala ta fada cikin ruwa domin ceto mijinta da kifi ke shirin cinyewa | Photo credit: Dailymail UK
Source: Facebook

Matarsa mai suna Margot Dukes Eddy mai shekaru 29 ta shige ruwan cikin hanzari ta janyo mijinta bayan ta hango yadda jini ya gauraye da ruwan, da kuma wani sashi na jikin kifin.

A yadda Christopher Aguanno ya bada rahoto, ba Eddy da matarsa kadai bane a cikin jirgin ruwan, har da iyayen matar tasa, da kanwar ta da kuma saurayin kanwar, wadanda suka fada cikin ruwan lokacin da kifin ya kawo harin.

KU KARANTA: Yadda wata budurwa 'yar Najeriya ta samu wata gagarumar kyauta daga wajen mai kudin duniya Bill Gates

Kamar yadda ofishin babban jami'in 'yan sanda na yankin ya ruwaito, an tafi da Eddy asibiti bayan an samu nasarar kwato shi daga bakin kifin da kimanin karfe 10:30 na safe.

An ce yaji munanan ciwuka duk da ba'a riga an fadi halin da yake ciki ba yanzu haka.

A yadda ofishin ya bayyana, wadanda suka gani da idanunsu sunce gaskiya kifin kato ne sosai saboda zai kai kafa 8 zuwa 10.

Bayaga Eddy, babu wanda yaji ciwo a cewar ofishin.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin cigaba da kiran Sallah a wani Masallaci da aka hana a kasar Jamus

Yayin da wata ke kokarin ceto mijinta ta kowanne hali, a daya bangaren kuma hira ce ta barke tsakanin wani mahaifi da karamar diyarsa wanda ya jawo asirin matarsa ya tonu har ta kai ga sanadiyyar mutuwar aurensu na shekara 14.

Bayan Steven ya dawo gida sai hira ta barke tsakaninsa da diyarsa har ya tsinci wata magana daga cikin hirarsu. Yarinyar ta sanar da mahaifinta cewa mahaifiyarta ta shiga gidan makwabta.

Mutumin ya cigaba da yiwa diyar tasa tambayoyi, har tace ma sa a lokacin da ta dawo gida ta fara neman mahaifiyar ta ta, sai makwabcinsu ya leko da kansa yace mata yanzu mahaifiyarta zata iso gareta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel