Yadda ubangidana yake daureni yana lalata da ni, yana bani magani da giya don kada in dauka ciki - 'Yar aiki

Yadda ubangidana yake daureni yana lalata da ni, yana bani magani da giya don kada in dauka ciki - 'Yar aiki

- Matashiyar mai aiki mai suna Balogun a jihar Legas ta bada labarin yadda ubangidanta ke lalata da ita

- A cewarta, a duk lokacin da matarsa ta fita aiki, yana daureta sannan ya sadu da ita kuma ya bata magani da giya

- Kamar yadda ta sanar da 'yan sanda, yana mata barazanar kisa idan har ta sanar da wani abinda ke faruwa da ita

Wata matashiyar budurwa da ke aiki a jihar Legas, ta zargi ubangidanta da yi mata fyade a cikin gidansa a duk lokacin da ya samu dama.

Matashiyar da aka gano sunanta Balogun, ta ce ubangidanta yana mata karfi da yaji inda yake saduwa da ita kuma yana tirsasata shan maganin hana daukar ciki bayan ya kammala.

Ta sanar da SaharaReporters cewa, ubangidanta ya kan daure mata hannu da kafafu idan yana son yin fyaden kuma yana barazanar kasheta.

"Lamarin ya fara yayin da matarsa ta koma bakin aiki bayan kullen korona. Ubangidan ya kirani inda ya daureni tare da yin lalata da ni.

"A duk lokacin da ya yi min fyaden, yana bani magani da giya saboda kada in dauka ciki. Ubangidana yana barazanar kasheni idan na sanar wa wani. 'Yan sanda sun kama shi kuma na basu maganin da yake bani," Balogun tace.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, an mika wa 'yan sanda koken kuma sun kama shi, amma babu dadewa suka sakesa ba tare da gurfanar da shi ba.

Balogun, wacce 'yar asalin Abeokuta ce daga jihar Ogun, ta je aiki a jihar Legas don samun abinda za ta taimaki rayuwarta da shi.

Ta ce tana bukatar a yi mata adalci a kan yadda ubangidanta ya dinga cin zarafinta.

KU KARANTA: Yadda sama da 30m ta yi batan-dabo a ma'aikatar noma ta jihar Kano

Yadda ubangidana yake daureni yana lalata da ni, yana bani magani da giya don kada in dauka ciki - 'Yar aiki
Yadda ubangidana yake daureni yana lalata da ni, yana bani magani da giya don kada in dauka ciki - 'Yar aiki. Hoto daga @vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotuna da tarihi: Manyan Sarakuna 8 da arewa ta rasa a cikin shekaru 20

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke garin Dutse a jihar Jigawa a ranar Laraba, ta bada umarnin adana mata wani makaho mai shekaru 60 mai suna Muhammad Abdul.

Ana zarginsa da yunkurin yin luwadi da dan jagorarsa, lamarin da yasa aka bukaci adanasa a gidan gyaran hali.

Alkalin kotun majistaren mai suna Akilu Isma'il, wanda ya umarci a adana masa Abdul a gidan gyaran halin, ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel