Kotu ta bada umarnin cigaba da kiran Sallah a wani Masallaci da aka hana a kasar Jamus

Kotu ta bada umarnin cigaba da kiran Sallah a wani Masallaci da aka hana a kasar Jamus

- Za'a cigaba da kiran sallar juma'a a masallacin Jamus bayan dakatar da hakan da akayi na wani lokaci

- Kotu ta dakatar da kiran sallar ne tun bayan wasu ma'aurata kiristoci da suka yi korafi cewa kiran sallar yana shiga hakkinsu

- Kotun tace a shari'ance, kiran sallah baya cutar da mai sauraro don haka a cigaba

A ranar Laraba, wata kotu dake birnin Munster a yammacin kasar Jamus ta bada damar cigaba da kiran sallar juma'a a wani Masallaci

Hakan ya biyo bayan daukaka karar da yan garin Oer-Erkenschwick suka yi akan hukuncin hana kiran sallah da akayi musu, suna neman rangwame.

An haramta kiran Sallah a Masallaci a kasar Jamus bayan wasu ma'aurata sun yi korafi kan ana shiga hakkinsu
An haramta kiran Sallah a Masallaci a kasar Jamus | Photo credit: DW
Source: Facebook

KU KARANTA: 'Yan daba sun tare matar aure, sun yi awon gaba da takin da take tafe da shi

Alkalin kotun mai suna Annette Kleinschnittger ya ce "Dole ne kowacce al'umma ta amince da cewa wajibi ne wasu bangare su san yadda wasu suke yin harkokin su na bauta."

A wani zaman kotu da akayi a 2018, an dakatar da kiran sallah a masallacin juma'ar, tun bayan wasu Kiristoci wadanda gidansu ba shi da nisa da Masallacin suka yi korafi akan shiga hakkinsu da ake yi da kiran sallar.

Kotun ta Munster ta gano inda shari'a ta bawa kowa damar yin addininsa, sai dai babu dokar da ta bawa wani damar matsawa wani yayi addininsa.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 25, mutum 20 sun raunata

Haka Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda hukumomin tsaro a kasar Rasha suka kama wani tsohon dan sanda dake daga hannu akan titi da ke ta tara al'umma yana ce musu shi Annabi isa ne ya dawo duniya.

Mutumin mai suna Sergie Torop, wanda mabiyansa suke kiran shi da suna Vissarion, ya kai shekaru 30 yanzu kenan yana jagorantar mutane kan wata akida a wata coci.

Kamar yadda jaridar The Guardian ta wallafa, sai da yan sanda dauke da makamai suka taru da jirgin sama kafin su samu su kama Sergei, inda mabiyansa suke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel