Zuhudu: Zulum ya dakatar da saka sunansa a wani aiki, ya saka sunan tsohon gwamna Kashim Shettima

Zuhudu: Zulum ya dakatar da saka sunansa a wani aiki, ya saka sunan tsohon gwamna Kashim Shettima

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi wa magabacinsa Sanata Kashim Shettima karamci ta hanyar saka wa wani lambu sunansa

- Da farko Ma'aikatar Muhalli na jihar ta sanar da saka wa lambun sunan Zulum ne amma ya ce a saka sunan Kashim Shettima don shine ya gina jami'ar

- Lambun yana cikin Jami'ar Jihar Borno ne da gwamnatin Sanata Kashim Shettima ta gina lokacin mulkinsa

Zuhudu: Zulum ya dakatar da saka sunansa a wani aiki, ya saka sunan tsohon gwamna
Zuhudu: Zulum ya dakatar da saka sunansa a wani aiki, ya saka sunan tsohon gwamna. Hoto daga @KashimSM
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum ya dakatar da saka sunansa a wani lambu a Ma'aikatar Muhalli na Jihar ta yi niyyar yi.

Ya bada umurnin a saka sunan magabacinsa Sanata Kashim Shettima a lambun da ke Jami'ar Jihar Borno kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"Kwamishina ya sanar da saka wa lambun Jami'ar suna na, na umurci a saka sunan magabacina.

"Shi ya kafa jami'ar don a haka ina son a saka wa lambun sunan mai girma Sanata Kashim Shettima saboda ayyukan da ya yi," in ji Zulum.

KU KARANTA: An huro wa tsohon minista wuta kan zarginsa da bada umurnin yi wa ma'aikatansa zigidir saboda N5,000

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da shirin fara shuka itatuwa 1,000,000 a jihar don magance ƙwararowar hamada da canjin yanayi.

Gwamnan ya ce ƙone daji da sare itatuwa ba bisa ƙa'ida ba da wasu mutane ke yi na barazana ga yanayin ƙasar kuma hakan na iya shafar samar da abinci.

Zulum ya nuna damuwarsa kan kwararowar hamada a jihar inda ya ce gwamnatinsa za ta yi ƙoƙarin magance matsalar.

A wani labarain daban, Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, ta amince da fitar da Dallar Amurka biliyan 1.95 domin ginin layin dogo da zai tashi daga Kano-Dutse (Jigawa)-Katsina-Jibia zuwa Maradi (Jamhuriyar Nijar).

Ministan Sufuri Rotimi Ameachi ne ya sanae da hakan yayin da ya ke yiwa manema labari jawabi a gidan gwamnati bayan taron Majalisar da Shugaba Buhari ya jagoranta a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel