'Yan bindiga sun kashe 'yan banga a Jigawa

'Yan bindiga sun kashe 'yan banga a Jigawa

- Ana zargin wani hatsabibin dan bindiga mai suna Bala Kama da laifin kashe wasu 'yan banga biyu a Jigawa

- Kakakin 'yan sanda na jihar Jigawa, Jinjiri Audu ya tabbatar da kisar gillar da ak yi wa 'yan bangan biyu a karamar hukumar Gwiwa

- Jinjiri Audu ya ce 'yan sanda sun kai sumame mabuyar 'yan bindigan sun kwato makamai amma har yanzu wanda ake zargin bai shigo hannu ba

'Yan bindiga sun kashe 'yan banga a Jigawa
'Yan bindiga sun kashe 'yan banga a Jigawa. Hoto @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa 'yan Najeriya ke korafi kan karin kudin wutar lantarki - Sanusi II

Rundunar 'yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da kisar wasu 'yan banga biyu a karamar hukumar Giwa a jihar.

Kakakin 'yan sanda, Audu Jinjiri, cikin wata sanarwar da ya fitar ya ce 'yan sanda sun kai sumame mabuyar 'yan bindigan sun kwato bindigu da harsasai.

Amma ya ce kawo yanzu ba a kama wadanda ake zargin ba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

"Yayin sumamen, daya daga cikin wadanda ake zargi mai suna Bala Kama na kauyen Tinkishi ya tsere.

"Wanda ake zargin ya kashe 'yan banga biyu kuma yana da hannu wurin satar babura da fashi a garin," a cewar kakakin 'yan sandan.

KU KARANTA: Fitar da bidiyon lalata na budurwa ya saka ango ya fasa aurenta a Sokoto

Mista Jinjiri ya ce kwamishinan 'yan sanda na jihar, Usman Gomma ya bada umurnin a bincike unguwan wanda ake zargin don dakile yaduwar bindigu.

Ya ce bayan sumamen da 'yan sanda suka kai wani rugan Fulani na Kabaka da ke karamar hukumar Gwiwa, "Yan sandan sun gano AK 47 biyu, wuka biyu, alburusai da harsashi."

"Ana zargin lauyi da samfurin harsashin da aka gano wurin da aka kashe 'yan bangan biyu ya yi kama da wadanda aka gano a rugar.

"Sashin binciken manyan laifuka CID tana zurfafa bincike yayin da ake kokarin kamo wanda ake zargin," in ji Jinjiri.

A wani labarin daban, mahalarta wani taron rana guda da aka yi a ranar Litinin a Katsina sun bukaci mazauna jihar su rika kare kansu duk lokacin da 'yan bindiga ko wasu miyagu suka kai musu hari.

Sun roki mutane su dena bari sai aikin samar da tsaro a hannun jami'an tsaro su kadai kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel