'Yan sanda sun kama wani Bature da yake ikirarin cewa shi Annabi Isah ne ya dawo duniya

'Yan sanda sun kama wani Bature da yake ikirarin cewa shi Annabi Isah ne ya dawo duniya

- Sergei Torop, wanda mabiyansa sukafi sani da Vissarion, ya kai shekaru 30 yana jagorantar wata akida

- An kama tsohon dan sandan kan titin tare da wasu shugabannin akidar bayan an zarge su da amsar kudaden al'umma da kuma dulmiyar dasu

- Mutumin mai shekaru 59 ya rasa aikinsa tun 1989, daga baya yayi ta ikirarin an tadashi a matsayin Jesus

Hukumomin tsaro a kasar Rasha sun kama wani tsohon dan sanda dake daga hannu akan titi da ke ta tara al'umma yana ce musu shi Annabi isa ne ya dawo duniya.

Mutumin mai suna Sergie Torop, wanda mabiyansa suke kiran shi da suna Vissarion, ya kai shekaru 30 yanzu kenan yana jagorantar mutane kan wata akida a wata coci.

'Yan sanda sun kama wani Bature da yake ikirarin cewa shi Annabi Isah ne ya dawo duniya
'Yan sanda sun kama Bature da yake ikirarin cewa shi Annabi Isah ne ya dawo duniya | Sky News
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar The Guardian ta wallafa, sai da yan sanda dauke da makamai suka taru da jirgin sama kafin su samu su kama Sergei, inda mabiyansa suke.

An kama shi ne, tare da wasu shugabannin akidar su, in da ake tuhumar su da amsar kudaden jama'a da kuma dulmiyar dasu akan hanyar karya.

KU KARANTA: Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata

'Yan sanda sun kama wani Bature da yake ikirarin cewa shi Annabi Isah ne ya dawo duniya
'Yan sanda sun kama wani Bature da yake ikirarin cewa shi Annabi Isah ne ya dawo duniya | Photo: Sky News
Asali: UGC

Mutumin mai shekaru 59 da haihuwa, ya rasa aikinsa tun a shekarar 1989 daga baya ya fara ikirarin dawowa aka yi dashi duniya.

Sergei na da mabiya a nan Rasha da sauran kasashe a fadin duniya kamar yadda jaridar the Guardian ta ruwaito.

Mabiyansa kamar yadda rahotanni suka zo, suna saka sutturu masu nauyin gaske da kuma haske, sannan kirgar shekarunsu ya fara daga 1961, shekarar da aka haifi Vassarion.

Bikin kirsimeti yana zuwa musu 14 ga watan Janairu na kowacce shekara, zagayowar ranar haihuwar Sergei.

Ba'a barinsu su ci duk wani abu da aka hada da nama, shayi da alkama.

'Yan sanda sun kama wani Bature da yake ikirarin cewa shi Annabi Isah ne ya dawo duniya
'Yan sanda sun kama wani Bature da yake ikirarin cewa shi Annabi Isah ne ya dawo duniya | Photo; Sky News
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan fashi sun yiwa wata mata fyade a gaban mijinta da 'ya'yanta a kasar Indiya

A kwanakin baya Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda shugaban kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenie, ya tabbatar da wallafa hoton Annabi Muhammad (SAW), a wata mujalla ta kasar Faransa mai suna CHarlie Hebdo.

Charlie Hebdo ta sake wallafa hoton Annabi Muhammad da Musulunci, wanda yayi sanadiyyar kai wani mummunan hari ga wannan mujalla a shekarar 2015.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 8 ga watan Satumba, Khamenie, ya ce, mujallar ta kasar Faransa ta aikata babban laifi ta hanyar zagin fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel