Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata

Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata

- Wani mutum dan kasar Pakistan ya siya wa matarsa fili a duniyar wata a matsayin kyautar aure

- Ya siyawa matar tasa filin ne a wata unguwa mai suna 'Sea of Vapour' a can duniyar wata

- Mutane da dama basu yarda ba, sai da sukaga takardun filin a hannunsa

Sohaib Ahmed mazaunin Rawalpindi ya siyawa matarsa fili a wata unguwa mai suna 'Sea of Vapour' a duniyar wata akan kudi dalar amurka arba'in da biyar ($45) a hannun hukumar duniya ta filayen duniyar wata.

Bayan Sushant Singh Rajput, jarumin fim din Indiya ya siyi filin a duniyar wata, shima dan Pakistan din yace baza'a barshi a baya ba, hakan ya sanya ya siyawa matar tasa a matsayin kyautar aure.

Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata
Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata | Photo Credit: Twitter/@HoorUlJannat5
Source: Facebook

Mutumin ya siyawa matar tashi filin mai girman filoti guda daya ne.

KU KARANTA: A shirye nake na biya ko nawa ne domin a cire ni daga cikin fim din 'Yan Shi'a - Yakubu Muhammed

Kamar yadda rahotanni suka riskemu, Sohaib Ahmed, mai shekaru 23 da haihuwa, mazaunin Rawalpindi ya siya wa matar tasa filin, kuma takardun filin yanzu haka suna nan a hannunsa.

A wata hira da SAMAA TV sukayi da Ahmed, yace ganin Sushant Singh Rajput ya siya filin yasa ya samu kwarin gwuiwar siya shima.

Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata
Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata | Photo Credit: Twitter/@HoorUlJannat5
Source: Facebook

Madiha, matar Ahmed ta bayar da labarin yadda kawayenta sukaki yarda lokacin da ta sanar dasu mijinta yayi mata wannan kyauta ta musamman.

"A lokacin da na fada wa mutane, kowa yasha wasa nikeyi sai da suka ga takarddun filin, mamaki ya kamasu," a cewar Madiha a lokacin da take hira da Samaa TV.

Bayaga Sushant, sanannun mutane kamar irin su Tom Cruise, Shah RukhKhan, John Travolta, Nicole Kidman suma duk suna da filaye a duniyar wata.

Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata
Wani ango ya jawo kace nace bayan ya siyawa amaryarshi fili a duniyar wata | Photo Credit: Twitter/@HoorUlJannat5
Source: Facebook

KU KARANTA: Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rai 1, sun sace mutum 10 a Nasarawa

Wani dan Najeriya mai suna Nwoke Agulu a ranar 21 ga watan Satumba, ya wallafa a shafinsa na Twitter yadda ya fasa auren wata budurwa saboda yawan kudin da yaga zai kashe akan auren.

Nwoke yace, duk soyayyarsu ta tashi a tutar banza a lokacin da ta sanar da shi ta kididdigar miliyan 4 da tayi idan lokacin aurensu yayi.

A cewar sa, matar ta ce zai fara tura mata Miliyan 1 a asusun bankin ta domin siyan kayan anko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel