Buhari ya amince a kashe $1.96bn don gina layin dogo daga Kano zuwa jamhuriyar Nijar
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a taron majalisar zartaswa ta kasa, ya amince a fitar da $1.96bn don gina layin dogo daga Kano zuwa Jamhuriyar Nijar
- Layin dogon, zai taimaka wajen safarar kayan masarufi da danyen mai daga Jamhuriyar Niger zuwa matatar mai da aka gina a tsakanin iyakokin kasashen biyu
- Ana sa ran layin dogon zai fara ne daga Kano, ya shiga Dambatta, Kazaure, Daura, Mashi, Katsina, Jibiya sannan ya tsaya a Maradi, Jamhuriyar Nijar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a fitar da $1.96bn don gina layin dogo da ya tashi daga Kano-Jigawa-Katsina-Jibia zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar.
Shugaba Buhari, ya amince da fitar da kudaden ne a ranar Laraba, a yayin zaman majalisar zartaswa ta kasa (FEC) a fadar shugaban kasa, Abuja.
KARANTA WANNAN: Buhari ya nada Abba Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM
Haka zalika, FEC ta amince a fitar da N745.2m don daukar hayar masu binciken kudi guda 8 da za su binciki badakalar kudi a hukumar bunkasa Niger Delta (NDDC).
Haka zalika, majalisar ta amince a fitar da N12.088bn domin bayar da kwangilar aikin hanyar Umuahia/Bende/Ohafia, mai tsawon kilomita 45.
KARANTA WANNAN: Daliban kwalejin KPS 5, da mutane 18 sun mutu a fashewar tankar fetur a Kogi
Ministan zirga zirga, Rotomi Amechi, da takwaransa na Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fasola, da na harkokin Niger Delta, Sanata Godswill Akpabio da na Ma'aikatar Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, suka bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron.
Da ya ke karin haske kan layin dogon, Ministan zirga zirga, Rotimi Amechi ya ce ma'aikatarsa ta gabatar da bukatu guda biyu, kuma majalisar ta amince da su.
A cewar sa: "Bukatu biyu ma'aiatar zirga zirga ta gabatarwa majalisar: Na farko bukatar kwangilar tsarawa, hadawa, da kawowa da gwajin taragon jirgi mai daukar kaya masu nauyin ton 150.
"Wannan ya faru sakamakon wani hatsari da aka samu akan taragon. Komai zai ci N3,049,544,000. Majalisar zartaswar ta amince da wannan bukata.
"Bukata ta biyu ita ce ta bayar da kwangilar gina layin dogo wanda zai ratsa daga Kano-Katsina-Jibia zuwa Maradi a Jamhuriyar Nigeria, da kuma zuwa Dutse, birnin Jigawa.
"Aikin gina layin dogon, zai ci kudi har $1,959,744,723.71, inda a ciki akwai harajin kaso 7.5 na VAT," a cewar Amaechi.
Rahotanni sun bayyana cewa layin dogo daga Kano a Nigeria zuwa garin Maradi a Jamhuriyar Nija na da tsayin kilomita 248, kuma zai ratsa ta shiyyoyi daban daban na Arewa.
Kwangilar gina layin dogon wanda aka so yinsa a shekarar 2018, zai hada akalla birane 7 na Nigeria da kuma birni daya na Jamhuriyar Nijar.
Ana sa ran zai fara ne daga Kano, ya shiga Dambatta, Kazaure, Daura, Mashi, Katsina, Jibiya sannan ya tsaya a Maradi, Jamhuriyar Nijar.
Idan aka kammala gina shi, zai taimaka wajen safarar danyen mai daga Jamhuriyar Niger zuwa matatar mai da aka gina a tsakanin iyakokin kasashen biyu.
Garin da aka gina matatar man, yana makwaftaka da jihar Katsina, kuma sai da aka cimma yarjejeniya tsakanin Nigeria da Nijar kafin aka gina matatar man.
A wani labarin, An nada Farfesa Abba Isa Tijjani a matsayin sabon shugaban hukumar gidajen ajiye kayan tarihi ta kasa (NCMM) Shugaban kasa.
Muhammadu Buhari ne ya amince da nadin Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM, wanda ya daga darajar masanin ilimukan daga Malami zuwa Shugaba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng