A shirye nake na biya ko nawa ne domin a cire ni daga cikin fim din 'Yan Shi'a - Yakubu Muhammed

A shirye nake na biya ko nawa ne domin a cire ni daga cikin fim din 'Yan Shi'a - Yakubu Muhammed

- Jarumin fina-finai na Kannywood, Yakubu Mohammed, ya nuna dana sanin sa akan fitowa a wani fim din Nollywood na 'yan shi'a mai suna "Fatal Arrogance"

- Jarumin ya nema masu fim din su fitar dashi a wurare 6 da ya bayyana, zai biya duk wata asarar da hakan zai jawo kamar yadda doka ta tanada

- Yace babu wanda ya kai masa hari, amma yasha caccaka da zage-zage har da alawadai a kafafen sada zumunta na zamani

Jarumin shirya fina-finai na Kannywood, Yakubu Mohammed, ya nuna dana sanin fitowa a wani fim din Nollywood na 'yan shi'a mai suna "Fatal Arrogance"

Fitaccen jarumin nan na kudancin Najeriya, Pete Edochie ya fito a matsayin jagora a shirin fim din da akayi a jihar Enugu, wanda Anosike Kingsley Orji ya dauki nauyi.

A shirye nake na biya ko nawa ne domin a cire ni daga cikin fim din 'Yan Shi'a - Yakubu Muhammed
A shirye nake na biya ko nawa ne domin a cire ni daga cikin fim din 'Yan Shi'a | Photo Credit: Instagram page, @yakubumohammed
Asali: Facebook

Ranar Talata kungiyar IMN suka wallafa a shafinsu na kafar sada zumunta na Facebook cewa: "hakika mun sha mamakin ganin yadda fim din ya nuna mabiya akidar Shi'a da kuma shugaba Sheikh Ibrahim Zakzaky a matsayin yan ta'adda."

A hirarsa da BBC Hausa, Mohammed yace yayi dana sanin fitowarsa a fim din, duk da yayi kokarin gyarawa masu shirya fim din abubuwa da dama ganin cewa akwai mutanen da ransu zai sosu idan suka kalli fim din, musamman yan arewacin Najeriya.

"Ban taba tunanin haka sauran shirin fim din zasu kasance ba, saboda a wurare 6 na fito. A cikin fim din harbi na akayi na mutu.

KU KARANTA: Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje

"Fim din ya nuna gumurzun 'Yan Shi'a da sojojin Najeriya da ya faru a Zaria, inda aka kashe mutane da dama. A lokacin da na karanta labarin, babu wata suka da aka yiwa Musulunci, amma kunsan labari ya kan canja, kuma hakanne ya faru.

Mohammed ya kara da cewa, ya bukaci mai shirya fim din ya cire duk wani wuri da ya fito, kuma a shirye yake da ya biya duk wata asarar da hakan zai jawo.

"Na ce wa mai shirya fim din, ya cire duk inda na fito a fim din kuma a shirye nake da in biya duk wata asara da hakan zai jawo, kamar yadda doka ta tanada."

A cewar jarumin, wata kungiya mai zaman kanta ce ta dauka nauyin fim din.

"Tabbas babu wanda yayi yunkirin kai min hari, amma naji yadda mutane ke ta zagina a kafafen sada zumuntar zamani saboda na fito a fim din."

Ya kara da cewa "Gaskiya akwai wuraren da duk musulmi zai ji ba dadi idan ya kalla. Akwai hoton Pete Edochie yana tafe cikin shiga irin ta musulmai, da kwalbar giya da kuma budurwa a gefensa."

"A gaskiya nayi dana sanin fitowa a fim dinnan."

KU KARANTA: Sabon hari: 'Yan bindiga sun halaka rai 1, sun sace mutum 10 a Nasarawa

Haka shi ma jarumin da ya fito a matsayin El-Zakzaky a cikin fim ya bayyana cewa rayuwar shi na cikin hadari domin kuwa ana ta faman yi masa barazanar kisa.

Kungiyar IMN sunce suna zargin hukumar sojin Najeriya da daukar nauyin fim din nan mai suna "Fatal Arrogance" saboda suyi kokarin rufe laifinsu na kisan wulakancin da suka yiwa 'yan Shi'a 348 a watan Disambar shekarar 2015.

Haka kuma kungiyar ta caccaki Pate Edochie sakamakon fitowa a matsayin El-Zakzaky a cikin sabon fim din. Inda jarumin da bakinsa yace ana farautar rayuwarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel