Zamfara: Yadda dan majalisa ya gwangwaje tsoffin malamansa da sha tara ta arziki

Zamfara: Yadda dan majalisa ya gwangwaje tsoffin malamansa da sha tara ta arziki

- Alhaji Kabiru Amadu Mai Palace dan majalisa ne da ke wakiltar mazabar Gusau da Tsafe a majalisar wakilan tarayya

- Dan majalisar ya gwangwaje tsofaffin malamansa na makarantun firamare, sakandare da Islamiyya da sabbin babura

- Ya ce, duk da sakamakonsu na wurin Allah, dole ne ya nuna musu jinjina a kan rawar da suka taka a rayuwarsa

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gusau da Tsafe a majalisar wakilai, Kabiru Amadu Mai Palace, ya gwangwaje malamansa da sabbin babura 10.

Malaman da ya bai wa wannan kyautar sun hada da tsoffin malamansa na firamare, sakandare da na Islamiyya, wadanda suka koyar da dan majalisar.

A yayin jawabinsa, Alhaji Mai Palace ya ce wannan dabarar ta zo mishi ne bayan tunawa da yayi da rawar da malaman suka taka wurin inganta rayuwarsa.

Kamar yadda yace, duk da sakamakon malaman na wurin Allah, akwai bukatar a kyautata musu da wasu abubuwan bukata na rayuwa.

Alhaji Kabiru ya ce, zai cigaba da tuntubarsu domin neman shawarwarin mulki da rayuwarsa baki daya, Daily Trust ta wallafa.

Wani tsohon babban sakatare, Malam Salihu Anka, wanda shine mataimakin shugaban makarantar sakandaren da Kabiru ya halarta, ya ce wannan kyautatawar ce ta dace da duk wani dalibi mai hankali da ya samu nasara a rayuwarsa.

KU KARANTA: Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, ango ya fasa

Zamfara: Yadda dan majalisa ya gwangwaje tsoffin malamansa da sha tara ta arziki
Zamfara: Yadda dan majalisa ya gwangwaje tsoffin malamansa da sha tara ta arziki. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: An gano dalilin da yasa sojan da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa

A wani labari na daban, Fatihu Muhammad, mai wakiltar yankin Daura, Sandamu, da Maiadua a majalisar wakilai, ya yi barazanar yi wa wani talakansa dukan tsiya.

A wani faifen sauti da yanzu ya ke ta yawo, an ji Honarabul Fatihu Muhammad ya na yi wa wani Malam Abdulbasid Bello Mai’adua barazana. Jaridar Katsina Post ta ce wannan ‘dan majalisa ya kira Abdulbasid Bello Mai’adua a wayar tarho, inda ya fada masa cewa zai sa a ba shi kashi.

‘Dan siyasar ya shaidawa wannan Bawan Allah cewa idan har bai daina rubutu a game da shi a kan shafinsa na Facebook ba, zai yi maganinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel