Yadda sama da 30m ta yi batan-dabo a ma'aikatar noma ta jihar Kano

Yadda sama da 30m ta yi batan-dabo a ma'aikatar noma ta jihar Kano

- Hukumar karbar korafi ta jihar Kano ta sanar da yadda kudi har naira miliyan 30 ya yi batan-dabo daga ma'aikatar gona ta jihar

- Shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin-Gado, ya ce hukumar ke kula da gonakin gwamnati wadanda ake haya kuma su ke karbar kudin

- Ya tabbatar da cewa, babban abun zargin shine sakataren ma'aikatar wanda shine ke kula da shige da ficen kudade a hukumar

Hukumar karbar korafi ta jihar Kano ta sanar da cewa ta samu labarin wasu kudi sama da miliyan 30 da aka wawure a ma'aikatar noma ta jihar Kano.

Hukumar ta gano cewa, an wawure kudaden ne bayan wani korafi da ta samu daga wata kungiyar manoma mata ta jihar.

Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya tabbatar wa da BBC cewa ma'aikatar na karbar kudin haya daga masu amfani da kadarorin gwamnati kamar gonaki, to amma kudin ya yi batan-dabo.

Ya ce bayanai sun zo musu daga kungiyoyin manoma da suka hada da kungiyar mata manoma da ke jihar Kano.

Kamar yadda yace, daga bayanan ne suka gano cewa an amshe kudi har naira miliyan 30 da doriya, kuma basu a banki. Bayan fara binciken ne suka samu wasu miliyan bakwai da doriya daga ma'aikatar.

Shugaban hukumar yace babban abun zargi shine sakataren hukumar ma'aikatar noman, domin shine ke da ruwa da tsaki wurin shige da ficen kudade.

KU KARANTA: Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, ango ya fasa

Yadda sama da 20m ta yi batan-dabo a ma'aikatar noma ta jihar Kano
Yadda sama da 20m ta yi batan-dabo a ma'aikatar noma ta jihar Kano. Hoto daga Dawisu
Source: Twitter

KU KARANTA: An gano dalilin da yasa sojan da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa

Kotun shari'ar Musulunci ta jihar kano ta yanke wa Shariff-Aminu dan shekara 22 hukuncin kisa bayan an kama shi dumu-dumu da laifin batanci ga manzon Allah, a wata wakarsa da ta yi ta yawo a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp.

Alkali Aliyu Muhammad Kani yace wanda ake zargin zai iya daukaka kara matukar bai gamsu da hukunci da aka yanke masa ba.

"Ya riga ya daukaka kara," a cewar Ganduje a ranar Talata.

"Za'a cigaba da shari'a har kotun koli. A halin yanzu muna jiran hukunci ne kawai," inji Ganduje.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel