Sanata Ali Ndume ya koka akan kisan Kanal din soja da 'yan Boko Haram suka yi a Borno

Sanata Ali Ndume ya koka akan kisan Kanal din soja da 'yan Boko Haram suka yi a Borno

- Ana cigaba da ta'aziyyar marigayi Kanal Dahir Bako wanda yan boko haram suka kashe a jihar Borno

- Ali Ndume, Sanata mai wakiltar kudancin Borno, yayi ta'aziyyar marigayin sojan, yana jaddada shi a matsayin dan kasa nagari

- Ndume yace za'ayi rashin Bako saboda sadaukar da kansa da yayi domin kauda ta'addanci a Najeriya

Sanata Ali Ndume, dan majalisa mai wakiltar kudancin jihar Borno a majalisar dattawa, ya kai ta'aziyyar marigayi kwamandan sojoji Kanal Dahir Bako.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda yan Boko Haram suka ji wa marigayin mummunan rauni a wani hari da suka kawo a jihar ta Borno.

Sanata Ali Ndume ya koka akan kisan Kanal din soja da 'yan Boko Haram suka yi a Borno
Sanata Ali Ndume ya koka akan kisan Kanal din soja da 'yan Boko Haram suka yi a Borno
Source: UGC

Ya rasu ne a asibitin Maimalari Cantonment na Maiduguri inda yake jinyar munanan raunukan da 'yan Boko Haram din suka yi masa.

Bako shine wanda ya jagoranci wani sintiri a yankin Sabon Gari-Wajiroko kusa da Damboa lokacin da yan ta'addan suka kai masa hari.

KU KARANTA: Tsohuwa 'yar shekara 57 da ta kammala JS3 na sakandare tace tana so ta zama ma'aikaciyar lafiya

Sojojin Najeriya sunyi alhinin sanar da mutuwar sa ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, suna bayyana shi a matsayin babban jarumi a hukumar soji.

A wata takarda da ya fitar a ranar Talata, 22 ga watan Satumba, Ndume wanda shine shugaban kwamitin majalisar dattawan sojojin Najeriya, ya bayyana marigayin a matsayin dan kasa na gari.

Dan majalisar yace "Za'ayi kewar Bako sakamakon irin dagewa da kaiminsa wajen kawar da ta'addanci a arewa maso gabashin Najeriya," Za'ayi kewarsa kwarai, kuma mutanen Damboa, jihar Borno da kasa baki daya bazasu taba mantawa dashi ba." Cewar Ndume

KU KARANTA: Tirkashi: Karamar yarinya ta sanar da mahaifinta yadda mahaifiyarta ke lalata da makwabcinsu idan baya nan

Haka kuma shugaban kwamitin kula da rundunar sojin Najeriya, Sanata Mohammed Ali Ndume, na jam'iyyar APC da ke wakiltar jihar Borno ta Kudu, ya jinjinawa kokarin rundunar sojin Najeriya.

Ya sanar da cewa, suna iyakar kokarinsu wurin yaki da rashin tsaro a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabas na kasar nan, inda mayakan ta'addanci suka yi katutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel