Yadda rasuwar Sarkin Zazzau ta girgiza zukatan 'yan Kannywood

Yadda rasuwar Sarkin Zazzau ta girgiza zukatan 'yan Kannywood

- Al'ummar kasar Zazzau, arewacin Najeriya da kuma kasa baki daya sun fada alhini a ranar Lahadin da ta gabata

- Daukacin al'umma sun yi ta'aziyyarsa, har da manyan jarumai, mawaka da kuma furodusoshin Kannywood

- Mawaki Aminu Ala bai yi kasa a guiwa ba bayan ta'aziyyarsa, ya rera masa baituka masu cike da hikima

A ranar Lahadin da ta gabata kasar Zazzau ta tashi da babban tashin hankali na rashin balaraben Sarkinta, Alhaji Dakta shehu Idris.

Ya rasu a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita. Rasuwar sarkin ta jefa zukatan jama'a cikin alhini kasancewarsa Sarki na tsawo shekaru 45.

Masana'antar fina-finan Hausa ta shiga cikin alhini domin jarumai masu tarin yawa da ke ciki da wajen jihar Kaduna sun mika ta'aziyyarsu a kan rasuwar.

Jarumi Adam A. Zango ya wallafa ta'aziyyarsa inda ya bayyana cewa ya yi babban rashi.

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Allah Ya jikan Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris. Allah Yasa Aljanna ce makomarsa. Mun yi babban rashi”, a cewarsa.

Jarumin ya kara da cewa, "Ba zan taba mancewa da kai ba, Mai Martaba sarki Dokta Shehu Idris, Sarkin Zazzau."

Hakzalika, ba a bar jarumin, wanda ake yiwa lakabi da Sarki, ya ce, "Ina mika sakon ta'aziyyata ga iyalai da dukkan jama'an Zazzau. Allah ya jikan Alhaji Dokat Shehu Idris, yasa mutuwa hutu ce garesa."

Fitaccen daraktan masan'antar, Falalu Dorayi, ya wallafa ta'aziyyarsa a shafinsa na Instagram.

Ya ce, "Allah mai girma! Daga Allah muke, garesa za mu koma. Allah ya gafarta wa Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris. Allah ya yafe masa kurakuransa, ya haskaka kabarinsa."

Babban furodusa Naziru Auwal kuwa, cewa yayi, "Yankin arewacin Najeriya ta yi babban rashin jigo a kan rasuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris. Allah ya jikansa, ya sanya shi a Aljanna."

KU KARANTA: Zaben Edo: Jama'ar Edo sun bai wa masu magudin zabe kunya - Kwankwaso

Yadda rasuwar Sarkin Zazzau ta girgiza zukatan 'yan Kannywood
Yadda rasuwar Sarkin Zazzau ta girgiza zukatan 'yan Kannywood. Hoto daga Abdulaziz Umar
Source: Facebook

KU KARANTA: Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, ango ya fasa

A bangaren fitaccen mawaki Aminu Ala, ya wallafa ta'aziyyarsa yana cewa, "Allah ya kyautata makwancin Sarki Shehu Idris Mai Zazzau.

"Hidimtawa al'ummar Zazzau daga shekara 1975 zuwa 2020 da ka yi, Allah ya baka sakamako da Aljannah.

"Allah ya kyautata bayanka da alheri," yace. Ya kara da rera masa baituka cikin hikima kamar haka:

Rabbu don RahamarKa Ka sa a wanke shi da Almiski,

Rabbu don tausayinKa da kankara marashin sa Raki,

Rabbu don gafararKa Ka kankare zunubansa na aiki,

Rabbu don tausayinKa dukkan su’ali su zam masa sauki,

Rabbu sa kabbarinsa Min Raudhatun min riyadhul Hakki

A wani labari na daban, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Lahadi ya shugabanci ministoci da manyan jami'an gwamnati zuwa kasar Zazzau domin wakiltar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wurin jana'izar Sarkin Zazzau.

Daga cikin wakilan akwai ministar kudi, kasafi da tattali, Zainab Ahmed, ministan muhalli, Dr. Mahmud Mohammed da ministan sufurin jirgin sama, Sanata Hadi Sirika.

Hakazalika, daga cikin wakilan shugaban kasan akwai mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel