Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna)

Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna)

- Kungiyar kiyayye hakkin al'umma ta Joint Action Forum a Kano ta shirya zanga-zangar kin amincewa da karin kudin man fetur da lantarki

- Kungiyar ta yi kira da gwamnatin tarayya ta mayar da tsohon farashin litar man fetur na N86 ta kuma janye karin kudin lantarki da harajin VAT

- Kungiyar ta kuma yi kira ga hadaden kungiyar kwadago na kasa ta tabbatar gwamnatoci na biyan albashi mafi karanci na N30,000 a dukkan jihohi

Hukumomin tsaro da suka hada da 'yan sandan, 'yan sandan farar hula, DSS, da jami'an hukumar tsaro da NSCDC sun hana wasu 'yan Najeriya yin zanga-zanga a kan karin farashin man fetur, lantarki da haraji a kasar.

An fara zanga-zangar ne a kofar ofishin Kungiyar 'yan Jarida ta Kasa, NUJ, da ke Farm Centre Road a safiyar ranar Talata a Kano yayin da jami'an tsaro masu yawa suke wurin.

Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna)
Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben Edo: 'Yan daban da ke yi wa PDP aiki sun yiwa matar shugaban jam'iyyar mu duka - APC (Hotuna)

Wata kungiyar kare hakkin al'umma mai suna Joint Action Forum ce ta jagorancin zanga-zangar kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna)
Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

Sanarwar da shugaban kungiyar, Dr Musa Bashir da Sakatarenta, Abba Bashir Ahmed suka fitar ta yi kira da gwamnatin jihar ta mayar da farashin man zuwa N86 duk lita ta kuma mayar da tsohon farashin lantarkin.

"Muna neman a mayar da farashin man fetur daga N160 zuwa N86 kamar yadda ya ke a 2012, kana a janye karin wutar lantarkin da harajin VAT da aka yi nan take.

Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna)
Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

KU KARANTA: Mai gida ya kashe 'yar haya saboda N11,000

"Ya kamata gwamnati ta gyara matatun man fetur din kasar ta kuma gina sabbi domin a tabbatar man fetur ya yi araha.

Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna)
Tsadar rayuwa: Jami'an tsaro sun hana yin zanga-zanga a Kano (Hotuna). Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

"Ya kuma kamata a yi wa hukumomin tsaro garam bawul domin takaita laifuka kamar ta'addanci, harin 'yan bindiga, garkuwa da mutane da fashi."

Masu zanga-zangar sun yi kira ga Hadakar kungiyar kwadago ta tabbatar gwamnatoci suna biyan albashi mafi karanci na N30,000 a dukkan jihohin kasar.

A wani labarin, kun i cewa an nada tsohon jami'in tuntuba na Majalisar Tarayya, Sanata Muhammad Abba-Aji a matsayin Sakataren kungiyar gwamnonin yankin Arewa ta Gabas, NEGF.

Abba-Aji ya rike mukamin jami'in tuntuba a majalisar tarayya a zamanin mulkin shugaban kasa Umaru Yar'adua da Goodluck Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel