Zulum ya yi alhinin rasuwar Kanar Bako, Kwamandan sojin da Boko Haram ta kashe a Borno

Zulum ya yi alhinin rasuwar Kanar Bako, Kwamandan sojin da Boko Haram ta kashe a Borno

- Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum ya yi ta'aziyar rasuwar kwamandan sojojin Najeriya, Kanar Dahiru Bako da Boko Haram suka kashe

- Kanar Bako ya rasu ne sakamakon raunin da ya samu bayan harin kwantar bauna da 'yan ta'addan suka kai wa tawagarsa a karamar hukumar Damboa, jihar Borno

- Zulum ya bayyana bakin cikinsa game da rasuwar Bako, ya kuma ce al'ummar Borno ba za su taba mantawa da shi ba tare da yin addu'ar Allah ya gafarta masa

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya yi wa Rundunar Sojin Najeriya ta'aziyyar rasuwar Kanar Dahiru Bako da ya mutu sakamakon harin kwantan bauna da Boko Haram suka yi wa sojoji a Borno.

An kai wa Mista Bako hari ne a ranar 20 ga watan Satumba tare da tawagarsa yayin wani sintiri da suka tafi a Sabon Gari - Wajiroko a karamar hukumar Damboa.

Zulum ya yi alhinin rasuwar Kanar Bako, Kwamandan sojin da Boko Haram ta kashe a Borno
Zulum ya yi alhinin rasuwar Kanar Bako, Kwamandan sojin da Boko Haram ta kashe a Borno. Hoto daga Guardian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sultan Sa'ad Abubakar III ya nada sabbin hakimai 15 a Sokoto

Zulum, wanda cikin sakon da kakakinsa Isa Gusau ya fitar a Maiduguri a ranar Litinin ya ce sadaukarwar da babban sojan da sauran sojojin suka yi ba zai tafi a banza ba.

Ya ce: "Kowa ya sani ina son marigayi Kanar Bako kamar yadda mutane da dama ke son sa.

"Bako soja ne na gaskiya wadda ke yi wa sojojinsa jagoranci ba tare da fargaba ba saboda kishin kasa.

"Da izinin Allah, sadaukarwar da marigayi Kanar Bako da sauran jarumai kamarsa suka yi ba za ta tafi a banza ba.

KU KARANTA: Zaben Edo: 'Yan daban da ke yi wa PDP aiki sun yiwa matar shugaban jam'iyyar mu duka - APC (Hotuna)

"Rasuwar jaruman mu duk da abin bakin ciki ne yana kara nuna mana cewa sojojin mu da sauran masu tallafawa ba su da abinda ya fi kare kasarsu.

"Al'ummar Borno ba za su taba mantawa da marigayi Kanar Bako ba da sauran mutane kamansa. Muna addu'ar Allah ya yafe masa kurakurensa da sauran jarumanmu da suka rasu."

Gwamnan ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da bawa Rundunar Sojojin Najeriya goyon baya domin kawo karshen ta'addanci a jihar.

A wani labarin daban, kun ji an kama wani mai gidan haya, David Ntiero Okon saboda banka wa yar hayarsa wuta a Calabar, jihar Cross Rivers saboda ta gaza biyan kudin haya N11,000.

Abin ya faru ne a ranar Laraba a gida mai lamba 9, Ansa Ewa Street a garin Cobham da ke Bayside a Calabar ta Kudu kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel