Daukar mutane 774,000 aiki daga jihohi 36: Muhimmin bayani daga FG

Daukar mutane 774,000 aiki daga jihohi 36: Muhimmin bayani daga FG

- Gwamnatin tarayya ta ce ta kara wa'adin mako daya, damar karshe, don jihohi su samu damar turo sunayen masu cin gajiyar shirin SPW

- An tsara shirin SPW ne akan daukar mutane 774,000 daga kananan hukumomi 774 na fadin kasar, tare da biyan N20,000 ga masu cin gajiyar shirin a kowanne wata

- A ranar 1 ga watan Oktoba gwamnati tace za ta kaddamar da shirin, inda a mako mai zuwa, bankuna shida za su yiwa masu cin gajiyar rejistar asusu

Rahotanni sun bayyana cewa aski ya zo gaban goshi, a yayin da ake daukar mutane 774,000 a karkashin shirin gwamnatin tarayya na 'Special Public Works (SPW)'

Sai dai, har zuwa yanzu, wasu jihohin ba su samu damar kammala daukar ma'aikatan da aka basu dama ba, wanda ya sa aka kara masu wa'adin mako daya.

KARANTA WANNAN: Bayan cin zaben Edo: Obaseki ya aike da sako ga Tinubu, Oshiomhole da ire irensu

Ministan kwadago da daukar aiki na cikin gida, Festus Keyamo ya ce har yanzu ranar 1 ga watan Oktoba ita ce ranar da za a fara shirin.

Daukar mutane 774,000 aiki daga jihohi 36: Muhimmin bayani daga FG
Daukar mutane 774,000 aiki daga jihohi 36: Muhimmin bayani daga FG
Asali: Twitter

Ya zuwa ranar Litinin da ta zamo ranar karshe ta daukar aikin, jihohin Yobe da Ebonyi sun aika da sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin.

KARANTA WANNAN: Babu sauran APC, abu daya ke rike da jam'iyyar - Sanata Rochas Okorocha

A ranar Litinin, Keyamo ya ce, "Mun gudanar da taron hukumar daukar aiki ta kasa NDE, inda muka duba yiyuwar kara wasu kwanaki, don jihohi su aiko da sunayen mutanen su.

"Har yanzu muna fatan fara shirin a ranar 1 ga watan Oktoba. A yanzu dai muna fuskantar wasu matsalolin cikin gida, amma zamu magance su kafin lokacin...

"A mako mai zuwa ne zamu sanar da wakilanmu da zasu kaddamar da shirin a jihohinsu. Kuma bankuna 6 ne za a yi amfani dasu don tura kudi ga masu cin gajiyar shirin," cewar Keyamo.

An tsara shirin SWP ne domin daukar mutane 1,000 daga kowacce karamar hukuma 774 da muke da su a fadin kasar.

Kowane mai cin gajiyar shirin zai rinka samun albashin N20,000 har zuwa karshen shirin.

Masu cin gajiyar shirin za su yi ayyuka da suka shafi na gwamnati, kamar dai yadda hukumar NDE na kananan hukumominsu za su dora su akai.

A wani labarin, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da ire irensa, barazana ne ga demokaradiyyar Nigeria.

Obaseki ya bayyana hakan a ranar Talata a tattaunawa da shi cikin 'Shirin Safiya' na gidan talabijin din Arise TV, wata kafar watsa labarai ta jaridar THISDAY.

Asali: Legit.ng

Online view pixel