Abubuwa 5 da Obaseki ya fadi kafin zaben jihar Edo
- Zaben jihar Edo tun kafin isowarsa ya bayyana cike da rigingimu na siyasar cikin gida a jam'iyyar APC
- Bayan komawar Obaseki jam'iyyar PDP sakamakon rasa tikitinsa, an cigaba da jifan juna da kalamai kala-kala
- Tun kafin zaben, Gwamna Godwin Obaseki ya sha alwashin yi wa Adams Oshiomhole murabus a siyasance
Sanannen abu ne cewa zaben jihar Edo ya zo da rigingimu masu tarin yawa. Rigingimun sun fara da na cikin gida tsakanin tsohon Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da Gwamna Obaseki.
Bayan kamarin da rigingimun suka yi kuma aka hana Gwamna Obaseki tikitin takara a jam'iyyar APC, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.
Wannan lamarin yasa abokan adawan, wadanda a da abokan juna ne, suka dinga jifan junansu da maganganu kala-kala. Ga wasu daga cikin kalaman Obaseki ga manyan abokan hamayyarsa:
1. Na cancanci zarcewa saboda in cigaba da ayyukan cigaban da na fara - Obaseki
Gwamna Obaseki ya sanar da cewa, zarcewarsa abu ne mai yuwuwa. Ya sanar da makusantansa cewa, ya cancanci zarcewa, shiyasa yake nemanta.
Ya kara da cewa babu wanda ya isa yace ga wanda zai zama Gwamna baya ga Ubangiji, The Cable ta ruwaito.
KU KARANTA: Zaben Edo: Buhari bai taba amfani da karfin ikonsa wurin magudi ba - El-Rufai
KU KARANTA: Zaben Edo: Buhari bai taba amfani da karfin ikonsa wurin magudi ba - El-Rufai
2. Zamu yi wa Oshiomhole murabus a siyasance - Obaseki
A yayin da Gwamna Obaseki ke gangamin yakin neman zabensa a karo na biyu,, ya sha alwashin sai ya yi wa Oshiomhole murabus a siyasance.
Ya tabbatar da cewa, Oshiomhole ya raina jama'ar jihar Edo saboda yana kokarin kakaba musu wanda zai mulkesu, jaridar The Cable ta tabbatar.
3. Wannan zaben gasa ce tsakanina da Oshiomhole ba Ize-Iyamu ba - Obaseki
A gangamin neman zabe wanda Gwamna Godwin Obaseki ya ziyarci karamar hukumar Oredo ta jihar Edo ya sanar da hakan.
A nan ya tabbatar da cewa wannan zaben mai karatowa ba tsakaninsa bane da dan takarar jam'iyyar hamayya ba, tsakaninsa ne da Oshiomhole.
4. Ize-Iyamu kanina ne - Obaseki
Gwamna Obaseki ya tabbatar da cewa a matsayin kani ya dauka dan takarar babbar jam'iyyar adawa, Fasto Osagie Ize-Iyamu.
Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin da ya kai wa babban basaraken jihar ziyara, Oba na Benin, Ewuare II a fadarsa.
Ya sanar da basaraken cewa, Ize-Iyamu na matukar ganin girmansa, hakan ne yasa ba zai yadda wannan mutuncin nasa ya zube ba ta hanyar yin rikici yayin zabe.
5. Na daukar wa Ubangiji alkawari, babu jinin da zai zuba saboda neman tazarcena - Obaseki
Ana saura kwanaki kadan zaben jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya ce ya dauka alkawarin cewa babu jinin da za a zubar yayin da yake neman zarcewa.
Ya sanar da hakan ne yayin addu'ar zaman lafiya da suka yi bayan azumin kwana daya da suka yi na neman nasara da kuma zaman lafiya yayin zabe.
A wani labari na daban, jam'iyyar PDP ta zargi cewa ana takurawa tare da tsananta wa hukumar zabe mai zaman kanta don juya sakamakon zabukan da ke isowa na gwamnan jihar Edo.
Duk da wannan ikirarin, Premium Times ta tabbatar da cewa bata da wata shaida da ke bayyana hakan.
A wata takarda da sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya fitar a ranar Asabar, jam'iyyar ta zargi cewa tana sane da takurar da hukumar ke fuskanta domin sauya alkalumman zabe a yankunan ruwa na jihar domin APC ta lashe zaben.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng