Gwamna Obaseki ya aike wa da Ize-Iyamu sako mai muhimmanci

Gwamna Obaseki ya aike wa da Ize-Iyamu sako mai muhimmanci

- Gwamna Godwin Obaseki ya mika godiyarsa ga jama'ar jihar Edo a kan jaircewar da suka nuna tare da goyon baya

- Obaseki ya kara da mika goron gayyatarsa ga Osagie Ize-Iyamu tare da bukatarsa da ya zo su hada kai domin cigaban jihar

- Gwamnan, wanda ya kwatanta Ize-Iyamu da dan uwansa, ya ce jama'a sun riga zun bayyana zabinsu kuma lokaci yayi da za su hada kai

Gwamna Obaseki ya aika da sako mai matukar muhimmanci ga dan takarar jam'iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, bayan lallasa shi da yayi a zaben da ya gabata.

Gwamnan ya yi kira garesa da ya rungumi zaman lafiya tare da dawowa wurinsa domin kawo cigaba ga jihar baki daya.

A yayin tattaunawar da yayi da BBC a ranar Lahadi, 20 ga watan satumba, bayan bayyana shi a matsayin wanda yayi nasarar lashe zaben, Obaseki ya sanar da Ize-Iyamu cewa jama'a sun riga sun bayyana zabinsu.

Obaseki, wanda ya nuna tsananin mamakinsa a kan yadda jama'a suka fito tare da goyon bayan da ya samu daga jama'ar Edo, ya ce sakamakon zaben ya bayyanawa 'yan adawa karshensu.

KU KARANTA: Hotuna: 'Yan sanda sun damke mutumin da ya birne jikansa da rai

Gwamna Obaseki ya aike wa da Ize-Iyamu sako mai muhimmanci
Gwamna Obaseki ya aike wa da Ize-Iyamu sako mai muhimmanci. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zamfara: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 40

A wani labari na daban, Obaseki ya jinjinawa jama'ar jihar Edo a kan goyon bayan da suka bayyana a yayin da aka yi zaben.

Ya mika godiyarsa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, INEC, jami'an tsaro da sauran wadanda suka tabbatar da zaben ya tafi lafiya kalau.

Obaseki ya ce: "Jama'ar jihar Edo sun yi magana. Sun sanar da abinda ke ransu a bayyane. Mun godewa Ubangiji kuma garesa muka sadaukar da nasararmu.

"Muna godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kariya da ya bai wa damokaradiyya tare da bai wa INEC da jami'an tsaro damar yin aikinsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya bayyana.

”INEC da sauran jami'an tsaro sun nuna wa 'yan Najeriya da sauran duniya cewa za su iya zaben gaskiya da amana."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel