Matar da ta aike wa Trump wasika mai guba ta shiga hannun jami'an tsaro

Matar da ta aike wa Trump wasika mai guba ta shiga hannun jami'an tsaro

- Jami'an tsaro a kasar Amurka sun cafke wata mata da ake zargi da aike wa shugaba Trump wasika dauke da guba

- An kama matar a birnin New york kusa da wata gada da ke iyakar Peace, tana kokarin tsallaka kasar

- Ba wannan bane karon farko a kasar Amurka da aka taba tura wa shugaban kasa wasika mai dauke da guba ba

Wata mata da ake zarginta da aike da ambulan mai dauke da wasika mai guba, wacce ta tura ga gidan gwamnatin Amurka, ta shiga hannu.

Jami'an tabbatar da doka sun sanar da mujallar The Associated a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, cewa an kama matar a birnin New York.

An kama wasikar a makon da ya gabata kafin ta isa gidan gwamnatin Amurka.

Jami'an hukumar kwastam da bada kariya ga iyakar kasar da ke iyakar gadar Peace suka kamata. Sun ce dole za ta fuskanci hukunci. Har yanzu basu saki sunanta ba.

Wasikar da ta rubuta ga gidan gwamnatin Amurkan an yi ta daga kasar Canada, 'yan sandan kasar suka tabbatar.

An kama wasikar a wata ma'aikatar gwamnati ne kuma binciken farko ya bayyana cewa an yi ta ga shugaba Donald Trump ne.

Kamar yadda jami'aan suka tabbatar amma suka bukaci a boye sunayensu, sun ce binciken farko da aka yi an gano wata guba mai suna ricin ce a ciki.

KU KARANTA: PDP ta yi babban rashi, wani makusancin Dogara ya koma APC

Ba wannan bane karo na farko da aka fara tunkarar manyan jami'an kasar Amurka da wasika mai dauke da guba ba.

A 2018, an kama wani tsohon sojan ruwa da ya tura wasiku a cikin ambulan ga Trump da wasu makusantansa wanda ke kunshe da muguwar gubar.

An kama wasikun kuma babu wanda ya mutu sannan aka damke tsohon sojan.

A 2014, wani mutum daga yankin Mississippi an yanke masa hukuncin shekaru 25 a gidan yari, bayan ya aike wa Shugaba Barack Obama da jami'ansa wasiku masu guba.

Matar da ta aike wa Trump wasika mai guba ta shiga hannun jami'an tsaro
Matar da ta aike wa Trump wasika mai guba ta shiga hannun jami'an tsaro. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe manoma 2 a jihar Nasarawa

A wani labari na daban, 'yan Najeriya sunata zama abubuwan alfahari a wurare daban-daban na duniya.

Yanzu haka, tauraruwar Kikelomo Lawal wacce aka fi sani da "Kike" ke haskawa, wadda mai girma mataimakin shugaban kasa kuma shugaban lauyoyi na bankin 'yan kasuwa na kasar Canada (CIBC) ya bata babban matsayi.

Kafin samun wannan matsayin, ita ce shugabar lauyoyin Ombudsman kuma sakatariyar Interac Corp na tsawon shekaru 12 da watanni 8.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel