Bayan ya yiwa saurayin kanwarsa dukan tsiya, saurayin ya siyo mata sabuwar mota mai tsadar gaske a matsayin godiya

Bayan ya yiwa saurayin kanwarsa dukan tsiya, saurayin ya siyo mata sabuwar mota mai tsadar gaske a matsayin godiya

- Wani mutumi mai amfani da shafin Twitter mai suna @Shabzen yayi dana sanin dukan saurayin kanwarsa da yayi

- Bayan faruwar lamarin,saurayin ya siyowa budurwar tasa dalleliyar mota

- Mutumin yace dalilinsa na dukan saurayin kanwar tasa shine, ya ajiye motarsa a kofar gidansu

Akwai masu cewa, kudi baya siyan soyayya, amma kuma tabbas kudi yana canja tunanin zuciyoyi da dama.

Wani mutumi mai amfani da shafin Twitter mai suna @Shabzan ya wallafa wani rubutu a shafinsa inda yake bayyana yadda ya kama saurayin kanwarsa yayi masa dukan tsiya sakamakon ajiye motarsa da yayi a kofar gidansu.

A ranar Lahadi, 13 ga watan Satumba ne, saurayin ya wallafa wannan rubutu a shafinsa na Twitter, inda yake cewa "Saurayin da ya siya wa kanwata dalleliyar motar nan nayi wa dukan tsiya," ya saka hoton kanwar tasa jingine da motar.

Bayan ya yiwa saurayin kanwarsa dukan tsiya, saurayin ya siyo mata sabuwar mota mai tsadar gaske a matsayin godiya
Photo source: Twitter/@Shabzen
Source: Twitter

Yace saurayin kanwata ya siya mata dalleliyar mota. Yanzu haka, ina dana sanin dukan da nayi mi shi ranar da ya ajiye motarsa a kofar gidanmu, inda ya wallafa hotonsa dana kanwartasa.

Wannan rubutu da ya wallafa ya jawo cece-nace a shafin sada zumunta, a inda wasu suke cewa yayi hakan domin kare martabar kanwarsa ne, wasu kuma suka yi ta sukarsa, suna cewa gaskiya ya zake.

KU KARANTA: Yadda wani karamin yaro dan Najeriya ya kera jirgin sama wanda yake tashi

Wata mai tsokaci mai suna @ Cindypulukuhlu tace gaskiya gayen ya kara ma kanwar tasa daraja ne, nima ina tuna lokacin da yayuna suka karamin kima a idon saurayina lokacin da saurayina ke biya min kudin makaranta.

Wani kuwa ce mishi yayi, da dai kaja masa kunne, amma nasan yanzu idan yazo wurinta bazaka damu ba ai.

Ra'ayi dai ance riga ne, haka nan samari da 'yammata suka yi ta tofa albarkacin bakunansu. Wasu suna cewa yayi daidai, wasu kuma suna kushewa tare da jin haushin wannan danyen hukunci da yayi.

KU KARANTA: An bawa 'yar Najeriya mataimakiyar shugaban wani babban banki a kasar Canada

Haka ita ma wata budurwa ta jawo rabuwar kan mutane a shafin sada zumunta na Twitter, bayan ta bayyana cewa wani mutumi ya tura mata kudi har naira dubu hamsin (N50,000) saboda kawai ta mayar masa da martanin sakon da ya aika mata a shafin sadarwa.

Budurwar mai suna @_Matriach da ta wallafa hotunan hirar da tayi da mutumin da kuma sakon waya da aka aika mata na kudin da ya tura mata, ta ce: "Kai ina matukar alfahari da zama na mace."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel