An bawa 'yar Najeriya mataimakiyar shugaban wani babban banki a kasar Canada

An bawa 'yar Najeriya mataimakiyar shugaban wani babban banki a kasar Canada

- Bankin CIBC ya bawa Kikelomo wacce aka fi sani da "Kike" Lawal babban matsayi, inda zata dinga lura da bangarori biyu a bankin

- Kafin samun wannan matsayin, dama ta samu gogewa a harkar kudi a wurare daban-daban

- Wannan sabon matsayin nata zai bata damar kaiwa shugabannin bankuna da kuma shugaban kasa baki daya rahoto

Yan Najeriya sunata zama abubuwan alfahari a wurare daban-daban na duniya.

Yanzu haka, tauraruwar Kikelomo Lawal wacce aka fi sani da "Kike" ke haskawa, wadda mai girma mataimakin shugaban kasa kuma shugaban lauyoyi na bankin 'yan kasuwa na kasar Canada (CIBC) ya bata babban matsayi.

An bawa 'yar Najeriya mataimakiyar shugaban wani babban banki a kasar Canada
Kikelomo Lawal | Photos sources: CanadianLawyerMag/PaymentSource
Source: UGC

Kafin samun wannan matsayin, ita ce shugabar lauyoyin Ombudsman kuma sakatariyar Interac Corp na tsawon shekaru 12 da watanni 8.

Kikelomo ta rike matsayin babbar jagora ga Blake, Cassels & Graydon LLP na tsawon shekaru 5 da watanni 9.

KU KARANTA: Yadda wani karamin yaro dan Najeriya ya kera jirgin sama wanda yake tashi

Tayi karatunta a jami'ar birnin New York da kuma makarantar lauyoyi ta Harvard. Jaridar Bloomreg ta ruwaito cewa 'yar Najeriyar na da kwarewa sosai wajen aikinta, kuma bata da nuna wariya wajen jinsi, addini, ko kuma wariyar fata.

"Ms Lawal za ta zama mai lura da yanayin harkokin shige da fice na kudi a wannan banki, sannan kuma ita ce sakatariyar dake tsare sirri da manufofin shirye-shirye na wannan banki.

"Za ta shiga cikin kwamitin zartarwa na wannan banki, sannan za ta dinga bada rahoto, ga shugaban wannan banki baki daya," jaridar Bloomberg ce ta bayar da rahoton wannan sabon mukami da ta samu.

KU KARANTA: Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada

Shi kuwa fitaccen mawakin nan dan kasar Senegal dake zaune a kasar Amurka, Akon, yayi magana akan shirin shi na gina birni wanda za a sanyawa suna Akon City a kasar Senegal.

Da yake magana da manema labarai a wajen wani taro da aka gabatar ranar Litinin, 31 ga watan Agust, 2020, ya ce babban abinda ya sanya zai gina birnin shine domin mutanen Afrika dake kasashen Turai su dawo gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel