Zaben Edo: Buhari bai taba amfani da karfin ikonsa wurin magudi ba - El-Rufai

Zaben Edo: Buhari bai taba amfani da karfin ikonsa wurin magudi ba - El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi shaidar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan gaskiya

- Gwamnan ya tabbatar da cewa, shugaba Buhari ba ya amfani da karfin ikonsa wurin saka wa a yi magudin zabe

- Gwamnan ya ce sun saka rai da kujerar gwamnan jihar Edo, amma sati biyu zuwa uku kafin zabe suka cire

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba yin amfani da isarsa ba ta yadda bai dace ba.

El-Rufai ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin tsokaci a kan zaben gwamnan jihar Edo da aka yi a ranar Asabar da ta gabata, The Cbale ta tabbatar.

Godwin Obaseki, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben, ya kada Ize-Iyamu na jam'iyyar APC da tazara mai yawa.

A yayin jawabinsa a shirin Sunrise Daily, wani shiri na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya ce yana fatan APC za ta ci zaben.

Kamar yadda yace, alamu sun nuna cewa jam'iyya mai mulki ce za ta yi nasara har sai a makonni uku da suka gabata.

Ya ce, "Ba kamar sauran gwamnatoci da suka gabata ba, Buhari yana bari a bar zabin jama'a a yayin zabe.

"Mun so yin nasara. A gaskiya ina ta mana fatan nasara tare da sa rai har sai da makonni uku da suka gabata. A nan alamun faduwarmu ta bayyana."

KU KARANTA: Bayan shan mugun kaye, Ize-Iyamu na APC ya yi martani

Zaben Edo: Buhari bai taba amfani da karfin ikonsa wurin magudi ba - El-Rufai
Zaben Edo: Buhari bai taba amfani da karfin ikonsa wurin magudi ba - El-Rufai. Hoto daga The Cable
Source: Twitter

KU KARANTA: Zamfara: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 40

A wani labari na daban, Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, ya fitar da takarda bayan lallasa shi da Gwamna Obaseki na jam'iyyar PDP yayi a zaben da ya gabata.

Obaseki ya samu kuri'u 307,955 inda ya kayar da babban abokin adawarsa, Ize-Iyamu, wanda ya samu kuri'u 223,619.

A martanin da ya fitar bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da nasarar Obaseki, Ize-Iyamu ya mika godiyarsa ga magoya bayansa a kan kokarin da suka yi masa yayin zaben.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel