Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada

Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada

- Wata kungiyar taimakon gaggawa ta jihar Legas ( LASEMA) a Eti-osa ta taimaki wata mata wurin haihu a kasan gadar Ajah

- Kamar yadda labarin ya bayyana, matar mai suna Blessing, ta haihu duk da bata da gida kuma tana zama a kasan gada

- Kungiyar ta taimaka wa matar har ta haifi santalelen jaririnta lafiya kafin a kaita babban asibiti don cigaba da kulawa da lafiyarta

A ranar Asabar, 19 ga watan Satumba 2020, kungiyar taimakon gaggawa ta LASEMA ta kawo agaji ga wata ma'aikata da gobarar mai ta barke wa ranar juma'a, 18 ga watan Satumba 2020 a Anthony Inward Gbagada domin gudun kada wata gobarar ta kara barkewa.

Ana cikin Wannan hargitsin, 'yan kungiyar LASEMA suka taru a Eti-Osa, kasan gadar Ajah domin daukar wani mataki na gudun barkewar wata gobarar sakamakon rufe gadar ta uku da aka yi, daganan suka amshi haihuwar jaririn.

Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada
Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada
Source: Facebook

KU KARANTA: Zargin garkuwa da mutane: Alkali ya bukaci a adana masa mata da miji a gidan yari

Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada
Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada
Source: Facebook

Blessing Emmanuel matace mara galihu yar shekaru 35 da haihuwa 'yar asalin jihar Cross River.

Bata da masauki kuma batada kowa a Legas. Dama tana watangarara ne a kasan gadar Ajah, sai kuma nakuda ta sameta. Kasancewar kungiyar LASEMA ce kadai zata iya bata taimakon gaggawa a lokacin da take yanke.

A matsayin LASEMA na kungiyar kula da lafiya wadda take tafe da kayan aikinta har kasan gadar Ajah a Eti-Osa, sai suka amshi haihuwar jaririn Mrs Blessing cikin sauki.

Duk da aikinsu ne taimakon rayukan jama'a, bayan sun amshi haihuwar sun dauka Blessing da jaririnta suka kai ta asibitin Island Maternity domin cigaba da kulawa da lafiyarsu.

KU KARANTA: PDP ta yi babban rashi, wani makusancin Dogara ya koma APC

Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada
Hotuna: Yadda ma'aikatan LASEMA suka taimakawa wata mata da bata da gida ta haihu a karkashin gada
Source: Facebook

Wani saurayi dan Najeriya ya hau shafinsa na Twitter, ya bayyana yadda matar yayansa da ya mutu ta takurawa rayuwarsa shekaru 20 da suka wuce, a lokacin da yake zaune da su.

Mutumin wanda yake da suna @Omodenden1 ya bayyana wannan rayuwa da ya fuskanta a baya a shafin nasa a matsayin sharhi da ya yiwa wani mai suna Segun Awosanya.

A cewar shi: "Kimanin shekaru 20 da suka wuce, matar yayana da nake zaune da ita ta taba cire takalminta, ta nuna ni da shi ta ce takalminta ya fini daraja. Yanzu kuma yayana ya mutu. Na zama lauya, kuma nine nake lura da danta. Amma ta kasa tinkara ta, sai dai ta turo dan aike idan tana son magana dani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel