Zaben Edo: Obaseki ya magantu bayan lallasa Ize-Iyamu na APC da yayi

Zaben Edo: Obaseki ya magantu bayan lallasa Ize-Iyamu na APC da yayi

- Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo ya sake lashe zabensa a karo na biyu wanda aka yi a ranar Asabar da ta gabata

- Kamar yadda gwamnan yace a jawabinsa na farko, ya mika godiyarsa ga takwarorinsa na jihohin PDP da suka kawo masa dauki

- Ya jinjinawa jama'ar jihar Edo wadanda yace kokarinsu ne ya kai shi ga sake komawa kujerarsa a karo na biyu

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sake nasarar lashe zaben jihar Edo a karo na biyu bayan zaben da aka yi na ranar Asabar da ta gabata.

Dan takarar jam'iyyar PDP din ya samu kuri'u 307,955 inda ya lallasa Fasto Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 223,619.

Sauran jam'iyyun siyasar da suka fito takarar amma basu bayyana kwazo ba su 12 ne. Sakamakonsu shine: AA – 107, ADC – 1,370, ADP – 2,374, APGA – 177, APM – 57, APP – 78, LP – 267, NNPP – 258, NRM – 573, SDP – 323, YPP – 132 da ZLP – 117.

Kamar yadda sakamakon ya bayyana daga bakin baturen zaben, Farfesa Akpofure Rim-Rukeh, shugaban jam'iar Effurun da ke jihar Delta, Obaseki ya samu nasarar lashe kananan hukumomi 13 daga 18 na jihar.

Kananan hukumomin da ya lashe sune: Orhionmwon, Igueben, Owan West, Oredo, Ikpoba-Okha, Esan West, Esan Central, Esan South East, Esan North East, Uhumwode, Egor, Ovia North East da Ovia South West.

Ize-Iyamu ya yi nasarar lashe kananan hukumomi biyar da ke yankin arewacin jihar. Su ne Akoko Edo, Etsako East, Etsako West, Etsako Central da Owan East.

Obaseki ya jinjinawa jama'ar jihar Edo a kan goyon bayan da suka bayyana a yayin da aka yi zaben.

Ya mika godiyarsa ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, INEC, jami'an tsaro da sauran wadanda suka tabbatar da zaben ya tafi lafiya kalau.

KU KARANTA: Dakarun soji sun damke fitaccen dan sara-suka da 'yan kungiyarsa 10 a Jos

Zaben Edo: Obaseki ya magantu bayan lallasa Ize-Iyamu na APC da yayi
Zaben Edo: Obaseki ya magantu bayan lallasa Ize-Iyamu na APC da yayi. Hoto daga The Nation
Source: UGC

KU KARANTA: Buhari ya tura wakilai Zaria, sun samu halartar jana'izar Sarki Shehu Idris

Obaseki ya ce: "Jama'ar jihar Edo sun yi magana. Sun sanar da abinda ke ransu a bayyane. Mun godewa Ubangiji kuma garesa muka sadaukar da nasararmu.

"Muna godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kariya da ya bai wa damokaradiyya tare da bai wa INEC da jami'an tsaro damar yin aikinsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya bayyana.

”INEC da sauran jami'an tsaro sun nuna wa 'yan Najeriya da sauran duniya cewa za su iya zaben gaskiya da amana."

”Ina godiya ga Gwamnan jihar Ribas, Gwamnan jihar Oyo, Gwamnan jihar Enugu da dan uwana Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a kan yadda suka tsaya mana.

"Ina godiya ga jam'iyyarmu ta PDP a kan damar da suka bani lokacin da nake matukar bukata, amma kuma jajircewa ce ta dawo da ni.

“Na rasa kalaman da zan yi wa magoya bayanmu godiya wadanda suka fito duk da barazana da sauran kalubalen da suka fuskanta. Kokarin jama'ar jihar Edo ne yasa muka yaki siyasar ubangida.

”Ina jaddada godiyata ga mataimakin Philip Shaibu. Muna godiya da gooyon bayanku," ya kara da cewa.

A wani labari na daban, jam'iyyar PDP ta zargi cewa ana takurawa tare da tsananta wa hukumar zabe mai zaman kanta don juya sakamakon zabukan da ke isowa na gwamnan jihar Edo.

Duk da wannan ikirarin, Premium Times ta tabbatar da cewa bata da wata shaida da ke bayyana hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel