Bayan shan mugun kaye, Ize-Iyamu na APC ya yi martani

Bayan shan mugun kaye, Ize-Iyamu na APC ya yi martani

- Dan takarar gwamnan jihar Edo, Ize-Iyamu, ya yi martani a kan mugun kayen da ya sha a hannun Obaseki

- Ize-Iyamu ya ce yana nazarin sakamakon zaben kuma babu dadewa zai sanar da matakinsa na gaba

- Dan takarar jam'iyyar APC a jihar Edo, ya mika godiyarsa ga magoya bayansa a kan kokarin da suka nuna yayin zaben

Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, ya fitar da takarda bayan lallasa shi da Gwamna Obaseki na jam'iyyar PDP yayi a zaben da ya gabata.

Obaseki ya samu kuri'u 307,955 inda ya kayar da babban abokin adawarsa, Ize-Iyamu, wanda ya samu kuri'u 223,619.

A martanin da ya fitar bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da nasarar Obaseki, Ize-Iyamu ya mika godiyarsa ga magoya bayansa a kan kokarin da suka yi masa yayin zaben.

Ya ce, "Sun jure abubuwa masu yawa har da wadanda suka hana su saka kuri'a."

Dan takarar APC din ya ce yana duba sakamakon zaben a halin yanzu kuma zai sanar da matakin dauka.

"Ina mika godiya ga magoya bayana wadanda suka jure dukkan sharri har da wanda ya hana su fitowa kada kuri'a. Sun bayyana goyon bayansu da kokarinsu yayin zaben.

"Ina tabbatar muku da cewa ina nazarin sakamakon tare da sauran 'yan jam'iyyar kuma za mu sanar da mataki na gaba," ya wallafa a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA: Da duminsa: Allah ya yi wa Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, rasuwa

Bayan shan mugun kaye, Ize-Iyamu na APC ya yi martani
Bayan shan mugun kaye, Ize-Iyamu na APC ya yi martani. Hoto daga Ize-Iyamu
Asali: UGC

KU KARANTA: El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza

A wani labari na daban, Gwamna Wike na jihar Ribas a daren Juma'a ya bayyana mamakinsa a kan tambayar da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, yayi masa.

Wike ya sanar da cewa babban dan sandan Najeriyan ya bukacesa da ya tattara komatsansa ya bar jihar Edo duk da yace ba a dauka wannan matakin a kan sauran gwamnonin APC da suka ziyarci jihar ba.

Gwamnan ya ce ya sanar da sifeta din 'yan sandan cewa, ya ziyarci jihar domin duba yadda zaben da za'ayi ranar Asabar zai tafi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng