Zaben Edo: An harbi ma'aikacin INEC, an raunata wani ma'aikacin wucin gadi
- Tun a ranar Asabar hukumar zabe ta kasa (INEC) ta fara sakin sakamakon zaben kujerar gwamnan jihar Edo
- Har ya zuwa wannan lokaci, jam'iyyar PDP ce a kan gaba da tazara mai yawan gaske daga sakamakon da aka kammala tattarawa
- Zaben kujerar gwamnan ya fi zafi a tsakanin gwamna mai ci, Godwin Obaseki, da babban abokin hamayyarsa, Osagie Ize-Iyamu, dan takarar APC
Wani ma'aikacin hukumar zabe ta kasa (INEC) ya na kwance a asibiti sakamakon mummunan raunin da ya samu bayan an harbeshi da bindiga a jihar Edo.
Babban baturen zaben gwamnan jihar Edo na karamar hukumar Etsako Central, Farfesa Godswill Alan Lukman, ya tabbatar da cewa an harbi ma'aikacin ranar Asabar a mazabar da ya ke aiki.
Farfesa Godswill ya sanar da hakan ne ranar Lahadi yayin da ya gabatar da sakamakon zaben karamar hukumar Etsako Central a cibiyar tattara sakamako ta jiha da ke Benin, babban jihar Edo.
Ya bayyana cewa ma'aikacin da aka harba bai mutu ba amma ya na cikin mawuyacin hali.
A cewar Farfesa Godswill, wasu 'yan dabar siyasa ne suka kawo farmaki wurin zaben, lamarin da ya haddasa barkewar rikici.
KARANTA: Yadda APC ke shan mugun kaye a hannun PDP a zaben jihar Edo
Ma su kada kuri'a sun tarwatse tare da gudun neman mafaka sakamakon rikicin da ya barke, a cewar Farfesa Godswill.
Bayan ma'aikacin da aka harba, 'yan dabar sun raunata wani ma'aikacin INEC na wucin gadi.
Baturen zaben ya bayyana cewa barkewar rikici a mazabar ya hana a cigaba da gudanar da zabe.
Ga wasu daga cikin sakamakon zaben kamar yadda INEC ta saki;
Karamar hukumar Igueben
PDP: 7,870
APC: 5,199
KARANTA: Jiya da yau: Muhimman abubuwa 5 da suka faru a ranar zaben Edo da wadanda ke faruwa a yanzu
Karamar hukumar Esan central
PDP: 10,964
APC: 6,719
Karamar hukumar Esan north-east
PDP: 13,579
APC: 6,559
Karamar hukumar Esan south-east
PDP: 10,565
APC: 9,237
Karamar hukumar Ikpoba Okha
PDP: 41,030
APC: 18,218
Karamar hukumar Owan east
PDP: 14,762
APC: 19,295
Karamar hukumar Etsako west
PDP 17,959
APC 26,140
Karamar hukumar Egor
PDP: 27, 621
APC: 10, 202
Karamar hukumar Esan west
PDP – 17,433
APC – 7,189
Karamar hukumar Uhunmwonde
PDP: 10,022
APC: 5,972
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng